Benuwai: Ɗan NYSC ya rasu bayan ‘yan bijilante sun lakaɗa masa duka a Buruku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani ɗan hidimar ƙasa na Hukumar NYSC ya rasu bayan zargin lakaɗa masa duka da wasu ‘yan bijilante suka yi a Ƙaramar Hukumar Buruku da ke Jihar Benuwai.

Hukumomi sun tabbatar da kamawa da tsare waɗanda zargi da hannu a laifin inda ake sa ran gurfanar da su.

Marigayin mai suna Ben Agir Une, wanda ɗan yankin Tongov ne a Ƙaramar hukumar Katsina-Ala, an kama shi ne a yayin wani sintiri cikin dare a yankin Anibros bisa zargin sa da a satar babur.

Shaidu sun ce, akan haka ne aka lakaɗa wa Une dukan kawo wuƙa da ya yi sanadiyyar ya samu mummunan raunuka a jikinsa.

Daga bisani aka garzaya da shi ofishin ‘yan sanda, inda jami’an tsaro suka shawarci da a garzaya da shi asibiti, inda a nan ne aka sanar da rasuwarsa.

Da yake tsokaci akan al’amarin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Buruku, Raymond Zege Aondoakura, ya yi alla-wadai da al’amarin, yana mai bayyana hakan a matsayin abin da aka yi bisa rashin tausayi da ba za su lamunta ba.

Ya bayyana cewa, ɗanyen aikin ya saɓa wa doka da ‘yancin ɗan-adam, inda ya tabbatar da cewa ba za a bari ya tafi kara zube ba.

By Babaji