Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
A wani yunƙuri na ƙarfafa rawar da mata ke takawa a harkokin gargajiya, Kuji Zambuk ya bai wa Hajiya Salamatu Wanbai Aliyu sarautar Kuji Gwatom, (Sarauniyar Zambuk) ɗaya daga cikin muhimman muƙaman gargajiya da ake bai wa mata a masarautar.
Salamatu Wanbai, wadda ta yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa, musamman a aikin jarida da harkokin siyasa, ta shafe shekaru tana aiki a gidan rediyo kafin ta tsunduma cikin siyasa, inda ta ci gaba da bada gudunmawa wajen cigaban al’umma.
Haka kuma tana rike da mukamin Alkebbar Kwadom, wanda ke kara nuna darajarta da tasirinta a tsakanin jama’a.
A yayin da ake bayyana dalilin nadin nata, Kuji Zambuk ya ce an yi la’akari da kwarewarta, jajircewarta da kuma kyakkyawar mu’amalarta da al’umma, wanda hakan ya sanya aka ga ta cancanci wannan sarauta mai daraja.
A madadin iyalai da ‘yan uwa, Habu Umar Dan Darman Zambuk ya nuna matukar godiya ga masarautar bisa wannan karamci, yana mai cewa zaben Salamatu ya zo a daidai lokacin da ake bukatar shugabar mace mai kishin al’umma domin ci gaba da daukaka wannan sarauta.
Ya kuma bayyana cewa suna shirin gudanar da bukukuwan gargajiya na cika wannan nadin, ciki har da wankan sarauta, cikin watanni biyu zuwa uku masu zuwa.
Da take jawabi bayan nadin, Salamatu Wanbai ta gode wa Kuji Zambuk da daukacin al’ummar yankin bisa amincewar da suka nuna mata, tare da yin alkawarin ba za ta ba su kunya ba wajen sauke nauyin da aka dora mata.
Sarautar Kuji Gwatom na daga cikin manyan mukamai na gargajiya da ake bai wa mata masu kima da nagarta a masarautar Zambuk.
Bikin naɗin ya samu halartar jama’a da dama, inda ‘yan rawa na gargajiya na al’ummar Tera suka kayatar tare da nuna farin ciki, yayin da aka gudanar da shagulgula cikin annashuwa.
