Gwamnatin Tarayya ta ninka kuɗin yaƙi da ta’addanci a kasafin 2026

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta ɗaga matakin yaƙi da ta’addanci ta fuskar shari’a, inda ta ware kimanin Naira biliyan 1.371 domin gudanar da shari’o’in da suka shafi ƙungiyar Boko Haram da sauran laifukan ta’addanci a kasafin kuɗin shekarar 2026.

Binciken da aka yi ya nuna cewa wannan sabon tanadi ya zarce kuɗin da aka ware a shekarar 2025, inda a wancan lokaci aka ware Naira miliyan 530 kacal, lamarin da ke nuna ƙaruwa mai yawa a ƙoƙarin gwamnati na tunkarar matsalar tsaro ta hanyar doka.

Wannan ci gaba ya fito ne bayan Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu kan dokar kasafin kuɗin 2026, wadda ta kai jimillar naira tiriliyan 68.32. Daga cikin wannan adadi, an ware kusan Naira tiriliyan 5.41 domin tsaro da kariyar ƙasa, wanda ya kai kusan kashi 7.9 cikin ɗari na gaba ɗaya kasafin.

Rahotanni sun nuna cewa rabin kasafin kuɗin na 2026 an karkata shi ne zuwa ayyukan raya ƙasa da gina muhimman ababen more rayuwa, yayin da bangaren shari’a ke samun ƙarin kulawa musamman wajen hukunta masu laifukan ta’addanci.

A cikin bayanan kasafin, an fayyace cewa kuɗin da aka ware don shari’o’in ta’addanci ya kai kusan kashi 14.1 cikin ɗari na dukkanin kuɗaɗen ayyukan raya da ke ƙarƙashin hedikwatar Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, wanda ya nuna muhimmancin da ake bai wa wannan fanni.

Idan aka kwatanta da shekarar 2025, jimillar kasafin hedikwatar ma’aikatar ya tashi daga naira biliyan 19.861 zuwa naira biliyan 23.685 a shekarar 2026, wanda ke nuna ƙarin kusan naira biliyan 3.825.

Masana harkar tattalin arziki da tsaro sun danganta wannan ƙaruwa da yawaitar shari’o’in ta’addanci, hauhawar kuɗin gudanarwa, da kuma rikitarwa da ke tattare da irin waɗannan shari’o’i a kotuna.

A baya-bayan nan, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya buƙaci ɓangaren shari’a da ya hanzarta sauraron ƙarar da suka shafi ta’addanci, satar mutane da sauran miyagun laifuka, yana mai jaddada muhimmancin hukunta masu aikata laifi cikin gaggawa domin dawo da zaman lafiya.

A watan Afrilu na 2026, Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu masu laifin ta’addanci hukuncin dauri har zuwa shekaru 20, yayin da gwamnati ke ci gaba da shari’ar manyan rukuni na mutane kusan 500 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci.

Haka kuma, gwamnati ta samu nasarar yanke hukunci kan mutum 386 daga cikin shari’o’i 508 da aka gabatar, yayin da wasu kaɗan aka sallama ko aka wanke su, sannan wasu kuma aka dage sauraron shari’arsu zuwa gaba.

Masu sharhi na ganin cewa wannan sabon tsari na ƙara kuɗi da ƙarfafa tsarin shari’a zai taimaka wajen rage rashin tsaro, tare da tabbatar da cewa masu tada zaune tsaye sun fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

By ukarofi