Sabon tsarin haraji zai iya durƙusar da masana’antar barasa, inji shugaban Breweries

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Gudanarwa kuma Babban Darakta na kamfanin barasa ta Nigerian Breweries, Thibaut Boidin, ya yi gargaɗi mai ƙarfi kan shirin Gwamnatin Tarayya na aiwatar da tsarin sitamfin haraji, wato taɗ stamp, yana mai cewa hakan na iya jefa masana’antar barasa cikin mummunar matsala tare da kawar da ribar kamfanoni gaba ɗaya.

Boidin ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai kafin babban taron shekara-shekara na kamfanin karo na 80 da aka gudanar a Legas, inda ya jaddada cewa duk da cewa ƙoƙarin gwamnati na ƙara tattara haraji abu ne mai muhimmanci, ya zama wajibi a tsara manufofi bisa la’akari da halin da masana’antu ke ciki domin kauce wa illa ga tattalin arziki.

“Sitamfin haraji wata hanya ce da gwamnatoci ke amfani da ita wajen sa ido kan kayayyakin da ake ɗorawa haraji kamar barasa, taba da abubuwan sha masu zaƙi, ta hanyar amfani da tambari ko lambobin dijital domin hana haramtacciyar sana’a da tabbatar da biyan haraji yadda ya kamata.

Sai dai Boidin ya bayyana cewa a Nijeriya, masana’antar barasa ba ta fuskantar matsalar haramtacciyar ƙera kaya da za ta sa a buƙaci irin wannan tsari.

Ya ce, “Ana amfani da taɗ stamp ne domin shawo kan haramtacciyar ƙera kayayyaki. An sanar da cewa za a fara amfani da shi a Nijeriya, amma hakan ya dace ne da masana’antun da ke fama da irin wannan matsala. A nan, babu irin wannan ƙera kaya ba bisa ƙa’ida ba.”

Ya ƙara da cewa, idan aka tilasta amfani da wannan tsari ga masana’antar barasa ta hukuma, zai haifar da mummunar illa ga harkokin kuɗi.

“Hasashenmu ya nuna cewa hakan zai iya rage ribar masana’antar da kashi 100 cikin 100. Mun yi lissafi, kuma sakamakon yana da girma ƙwarai,” inji shi.

A cewarsa, ba wai kawai ribar za ta ɓace ba, har ma gwamnati za ta rasa kuɗaɗen shiga daga wannan fanni, lamarin da zai iya haddasa durƙushewar masana’antar gaba ɗaya.

“Wannan na nufin gwamnati ba za ta sake samun kuɗaɗen shiga daga gare mu ba. Haka kuma, zai iya janyo rugujewar dukkan masana’antar,” ya ƙara da cewa.

Boidin ya kuma yi gargaɗin cewa illa daga wannan tsari na iya kai wa ga rasa ayyukan yi, inda ya ce sama da mutane miliyan uku da ke aiki kai tsaye da kuma a kaikaice a wannan fanni na iya shiga cikin haɗari idan samar da kayayyaki ya ragu.

Ya jaddada cewa masana’antu na buƙatar tsari mai daidaito da kwanciyar hankali wajen manufofin haraji, yana mai cewa sauye-sauyen da ba a tsara su da kyau ba kan iya rage kwarin gwiwar masu zuba jari.

Wani masani kan tattalin masana’antu a Legas, Dakta Bamidele Akinyemi, ya bayyana cewa kwanciyar hankali a dokoki yana da matuƙar muhimmanci ga irin wannan fanni da ke buƙatar jari mai yawa.

Ya ce, “Masana’antar giya tana aiki ne bisa dogon lokaci na zuba jari. Duk wata manufar da ta zo ba zato ba tsammani, musamman wadda ke ƙara kuɗin aiki ba tare da magance wata matsala ta kasuwa ba, na iya kawo tangarɗa ga ribar kamfanoni da kuma rage sha’awar saka jari nan gaba.”

Haka kuma, wata masaniyar manufofin haraji, Chioma Okoye, ta bayyana cewa duk da cewa tsarin “taɗ stamp” ana amfani da shi a duniya wajen tabbatar da tattara haraji, tasirinsa na dogara da yanayin ƙasa.

Ta ce, “Wannan tsari ya fi tasiri ne a wuraren da ake fama da haramtacciyar kasuwanci. Idan kuma an riga an tsara masana’antar yadda ya kamata, zai iya zama ƙarin nauyi ne kawai ba tare da wata fa’ida mai yawa ba, wanda hakan kan janyo hauhawar farashi da rashin inganci.”

Gargaɗin Boidin ya zo ne a daidai lokacin da kamfanin Nigerian Breweries ya dawo samun riba a shekarar 2025, bayan da ya yi asara a shekarar da ta gabata.

Kamfanin ya sanar da samun ribar kafin haraji ta naira biliyan 161.06, bayan da ya farfaɗo daga asarar naira biliyan 182.9 da ya yi a shekarar 2024, sakamakon ƙaruwa a kuɗaɗen shiga da kuma inganta tsarin kashe kuɗi.

By ukarofi