Rikicin Gabas ta Tsakiya na barazana ga bunƙasar tattalin arzikin Afirka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani sabon rahoton manufofi na haɗin gwiwa ya bayyana cewa, rikicin da ke ci gaba da ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya na iya rage yawan bunƙasar tattalin arzikin ƙasashen yankin nahiyar Afirka da kusan kashi 0.2 cikin ɗari.

Rahoton, mai taken “Tasirin Rikicin Gabas ta Tsakiya ga Tattalin Arzikin Afirka,” an gabatar da shi a birnin Washington DC, inda haɗin gwiwar Rukunin Bankin Raya Nahiyar Afirka, Hukumar Tarayyar Afirka, Hukumar Tattalin Arzikin Afirka ta Majalisar ɗinkin Duniya, Shirin Raya ƙasashe na Majalisar ɗinkin Duniya suka samar da shi.

A cewar rahoton, farfaɗowar tattalin arzikin Afirka daga girgizar tattalin arzikin duniya na baya-bayan nan na cikin hatsari sakamakon rikicin, musamman yayin da nahiyar ke ƙoƙarin murmurewa daga annobar COVID-19, yaƙin Russia–Ukraine da kuma tsadar kasuwancin duniya.

Babban masanin tattalin arziki kuma mataimakin shugaban AfDB mai kula da harkokin tattalin arziki, Kevin Urama, ya bayyana cewa muhimmancin mashigar Strait of Hormuz a harkokin sufuri da kasuwanci na duniya yana nuni da irin illar da duk wani tangarɗa a yankin zai iya haifarwa.

Ya ce, rikicin ya haifar da hauhawar farashin man fetur, abinci da takin zamani, tare da kawo cikas ga sarƙar samar da kayayyaki ta duniya, lamarin da ke ƙara dagula kasuwannin kuɗi da canjin kuɗaɗe.

Shi ma Sakatare Janar na ECA, Claver Gatete, ya bayyana cewa Afirka na matukar dogaro da yankin, yana mai cewa kashi 80 cikin ɗari na man da ake shigowa da shi nahiyar daga wannan yanki ne, yayin da rabin man da aka tace ma daga can yake fitowa.

A cewarsa, sama da ƙasashe 31 na Afirka sun riga sun fara fuskantar tangarɗar darajar kuɗinsu sakamakon wannan rikici.

Daga ɓangaren Hukumar Tatayyar Afrika, Francisca Belobe ta jaddada cewa duk da ƙalubalen, rahoton ya nuna juriyar tattalin arzikin Afirka a irin waɗannan lokuta na rikice-rikicen duniya.

Rahoton ya ba da shawarar cewa dole ne gwamnatocin Afirka su rungumi tsare-tsaren kuɗi masu tsauri da ingantaccen tsarin kula da hauhawar farashi, tare da kauce wa bayar da tallafi ba tare da tsari ba, wanda zai iya ƙara jefa ƙasashe cikin matsalar bashi.

Haka kuma, an buƙaci ƙasashen nahiyar su faɗaɗa hanyoyin samar da makamashi, abinci da kayayyakin masana’antu domin rage dogaro da kasashen waje, tare da ƙarfafa cinikayyar cikin gida musamman ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar Yankin Cinikayya na Bai ɗaya na Nahiyar Afirka.

Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ta yi kira da a haɗa kai domin kare nasarorin ci gaba da aka samu a nahiyar, tana mai jaddada muhimmancin cimma manufofin ci gaba masu ɗorewa.

Masu ruwa da tsaki sun kuma buƙaci ƙarin tallafi daga ƙungiyoyin duniya da cibiyoyin kuɗi domin taimakawa Afirka ta fuskanci wannan ƙalubale cikin nasara.

A ƙarshe, rahoton ya jaddada cewa haɗin gwiwa, ƙirƙire-ƙirƙire da saurin aiwatar da sauye-sauye ne za su taimaka wajen kare tattalin arzikin Afirka daga irin waɗannan girgiza na duniya.

By ukarofi