Zargin kamfanin Lafarge da tallafa wa ta’addanci ya jawo ayoyin tambaya kan ayyukansa a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukuncin da wata kotu a ƙasar Faransa ta yanke kan kamfanin siminti na Lafarge ya sake tayar da muhawara mai zafi, musamman a Nijeriya, inda kamfanin ke da manyan ayyukan masana’antu duk da ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta na tsawon lokaci.

Rahotanni sun nuna cewa, kotu a birnin Paris ta samu kamfanin da laifin tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta hanyar reshensu na Siriya, inda aka ce sun biya kuɗaɗen kariya ga ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai domin ci gaba da ayyukansu tsakanin shekarun 2013 da 2014. 

Wannan hukunci ya zama tarihi domin shi ne karo na farko da aka samu wani kamfani da irin wannan laifi a Faransa.

Kotun ta yanke wa kamfanin tara mai yawa, tare da kwace dukiyoyi, yayin da aka kuma yankewa wasu tsoffin manyan shugabanninsa hukuncin ɗaurin kurkuku. Cikin waɗanda abin ya shafa har da tsohon babban jami’in kamfanin, Bruno Lafont, wanda aka yanke masa hukuncin shekaru shida a gidan yari, da mataimakinsa Christian Herrault da aka yanke masa shekaru biyar.

Alƙalin shari’ar, Isabelle Prevost-Desprez, ta bayyana cewa kuɗaɗen da kamfanin ya biya sun taimaka wajen ƙarfafa ƙungiyoyin da suka haddasa hare-hare masu muni a cikin Siriya da ma wajen ƙasashen waje.

Ta ce, manufar biyan kuɗin ita ce kawai ci gaba da sarrafa masana’antar kamfanin, abin da ta kwatanta da wata irin “hulɗar kasuwanci” da ƙungiyar ISIS.

An gano cewa kamfanin ya biya sama da euro miliyan 5.5 ga ƙungiyoyi daban-daban ciki har da al-Nusra Front, duk kuwa da takunkumin da Tarayyar Turai ta ƙaƙaba a wancan lokaci. Har ila yau, an ruwaito cewa an kashe kuɗaɗe masu yawa domin samun damar shiga wuraren da ke ƙarƙashin ikon waɗannan ƙungiyoyi.

Sai dai duk da girman wannan hukunci, gwamnatin Nijeriya ba ta fito fili ta yi martani ba, lamarin da ke ƙara jawo damuwa daga masu sharhi, musamman ganin yadda ƙasar ke fama da matsalar ta’addanci daga ƙungiyoyi irin su Boko Haram da ISWAP.

Kamfanin na Lafarge, wanda yanzu ke ƙarƙashin Holcim Group, na ci gaba da gudanar da ayyukansa a Nijeriya ta hannun Lafarge Africa Plc, inda yake da manyan masana’antu a jihohi da dama kamar Ogun, Kuros Riba da Gombe. Wannan ya sa wasu ke tambayar ko ya dace a ci gaba da barin kamfanin yana aiki ba tare da cikakken bayani daga hukumomi ba.

Masana harkokin tsaro sun jaddada cewa ya zama wajibi hukumomi irin su ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro su fito su yi ƙarin haske domin kwantar da hankalin jama’a. Sun ce shiru kan irin wannan lamari na iya haifar da ƙarin zargi da rashin yarda daga al’umma.

A ƙarshe, wannan batu ya sake nuna muhimmancin da ke akwai wajen haɗa bunƙasar tattalin arziki da kuma tsaron ƙasa. Duk da yake saka hannun jari daga ƙasashen waje na da muhimmanci, masana na jaddada cewa bai kamata hakan ya zo da haɗarin da zai iya barazana ga tsaron ƙasa ba.

By ukarofi