Naɗin Murtala Garo: An ajiye ƙwarya a gurbinta — Hon. Kabiru Lalo

Spread the love

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU

An bayyana naɗin Hon. Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano a matsayin wanda ya dace, tare da cewa an “ajiye ƙwarya a gurbinta”.

Hakan ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin kodinetocin mataimakin gwamnan a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, Hon. Kabiru Ali Lalo, yayin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce al’ummar jihar da dama sun nuna farin ciki da wannan naɗi, duba da yadda Garo ke da farin jini musamman a wajen matasa.

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen bunƙasa siyasa da ci gaban jihar Kano. Ya ƙara da cewa za su ci gaba da zagayawa domin ƙara jawo masa goyon baya gabanin zaɓe mai zuwa.

Hon. Lalo ya yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa hangen nesansa wajen zaɓen Garo, yana mai cewa hakan zai kawo ci gaba mai ɗorewa a jihar.

By ukarofi