Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Taura da ke jihar Jigawa, Dakta Shu’aibu Hambali Zarga, ya bayyana cewa ƙaramar hukumar ta kashe kimanin Naira miliyan 68 wajen gyarawa da sabunta asibitin Taura, a wani yunƙuri na inganta harkokin kiwon lafiya a yankin.
Zarga ya ce wannan mataki na daga cikin manufofin ƙaramar hukumar na tabbatar da cewa al’ummar yankin suna samun ingantattun ayyukan jinya cikin sauƙi.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu asibitin na da likitoci uku da ke kula da marasa lafiya a kullum.
Shugaban ƙaramar Hukumar ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a Kaduna, a lokacin wani taron jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Gabas.
Hakazalika, ya bayyana cewa ƙaramar hukumar ta ɗauki ma’aikatan lafiya 118, waɗanda ke taimakawa wajen ba da kulawar farko ga marasa lafiya a sassa daban-daban na yankin.
Zarga ya jaddada cewa wannan ƙoƙari zai taimaka matuƙa wajen rage cunkoso a asibitin Taura tare da inganta lafiyar al’umma baki ɗaya.
Ya kuma yabawa gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa goyon baya da haɗin kan da yake bai wa ƙananan hukumomi domin bunƙasa harkokin lafiya da sauran ayyukan raya ƙasa.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga ma’aikatan lafiya da su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa da riƙon amana domin tabbatar da cewa al’umma na cin gajiyar waɗannan gyare-gyare.
