‘Yan bindiga sun kai hari coci a Ekiti, sun kashe fasto, sun yi garkuwa da masu ibada

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Mazauna garin Eda Oniyo da ke karamar hukumar Ilejemeje a jihar Ekiti sun shiga firgici a yammacin ranar Talata bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani coci yayin wani taron wa’azi a fili.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun afka cocin da ke wajen garin ne a lokacin da ake gudanar da wa’azin, inda suka kashe faston da ke jagorantar taron tare da sace wasu daga cikin masu ibada.

Majiyoyi daga cikin al’ummar yankin sun ce ‘yan bindigar, ɗauke da makamai, sun shafe wasu mintuna suna gudanar da harin kafin su yi awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba zuwa cikin daji da ke kusa.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda tsoron ramuwar gayya ta shaida cewa maharan sun zo da yawa kuma sun bude wuta yayin harin.

“Yammacin yau, wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani coci a wajen Eda Oniyo yayin wani shirin ibada. Sun yi garkuwa da mutane da dama, ciki har da tsofaffi da kananan yara.

“Sun harbe faston sannan suka tafi da masu ibadar zuwa cikin daji. Maharan sun zo da yawa kuma suna dauke da makamai masu nauyi,” inji majiyar.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba, amma lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin tsananin fargaba.

Wani babban jami’in gwamnati kuma mamba a kwamitin tsaro na jihar, wanda ya nemi a sakaya sunansa domin ba a ba shi izinin magana ba, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce tuni jami’an tsaro suka bazu a yankin domin farautar maharan, yana mai bayyana fatan cewa za a kubutar da wadanda aka sace lafiya.

“Eh, an yi garkuwa da wasu masu ibada a Eda Oniyo yau, amma hukumomin tsaro sun shiga lamarin. Gwamnati ta tura jami’an tsaro yankin kuma sun fara bin sahun maharan,” in ji shi.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda bai yi nasara ba, domin kiran waya da sakonnin da aka aikawa kakakin rundunar, Sunday Abutu, ba su samu amsa ba.

By ukarofi