Zargin cin amanar auren Sahabi da Farida Matawalle ya janyo tsegumi a soshiyal midiya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kafofin sada zumunta sun cika da tsegumi da muhawara bayan zargin cewa, Sahabi Liman, mijin Faridah Bello Matawalle, ya shiga wata badaƙalar cin amana makonni kaɗan bayan ɗaurin aurensu mai armashi.

Faridah ita ce ɗiyar Bello Matawalle, ƙaramin Ministan Tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Zamfara. An gudanar da aurenta da Sahabi ne ranar 6 ga Fabrairu, 2026, a Babban Masallacin ƙasa da ke a Abuja, cikin wani gagaruimin bikin aure da ya ja hankalin jama’a.

Rahotanni da ke yawo sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan wata mata mai suna Maryam ta wallafa wasu bayanai a shafukan sada zumunta da ke nuna akwai alaƙa a tsakaninta da Liman. Duk da cewa ba a tabbatar da sahihancin zargin ba, hakan ya haddasa ce-ce-ku-ce game da halin da auren yake ciki.

Wasu zarge-zarge sun kuma nuna cewa Mariam na da wata tsohuwar alaƙƙ da Liman, kuma ana zargin har bayan aurensa da Faridah, sun ci gaba da hulɗa a ɓoye.

Rahotanni na daban sun ce Faridah ta shiga wayar mijinta ne, inda ake zargin ta gano saƙpnni da ke nuna cin amana tsakaninsa da wata ƙawarta ta kusa, Mariam. Wannan iƙirari ya ƙara jefa batun cikin ruɗani, duk da cewa babu wata hujja a hukumance da ta tabbatar da labarin.

Lamarin ya haifar da martani kala-kala daga masu amfani da kafofin sada zumunta, inda wasu ke sukar abin da suka kira rashin amana, yayin da wasu ke ganin akwai buƙatar a yi taka-tsantsan wajen yarda da irin waɗannan zarge-zarge da ba a tabbatar da su ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga ɓangarorin da abin ya shafa domin tabbatarwa ko ƙaryata batun.

By ukarofi