Tsaro ya inganta a Fambeguwa, inji Babban Sarkin Kasuwa

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Sarkin Kasuwar Fambeguwa a ƙaramar hukumar Fambeguwa da ke jihar Kaduna, Alhaji Nura Usman Oska, ya bayyana cewa a halin yanzu yankin na samun ingantaccen tsaro, inda ya ce ba su da matsalar ’yan ta’adda ko masu aikata laifuka kamar yadda ake samu a wasu wurare.

Ya bayyana hakan ne a ofishinsa da ke Fambeguwa yayin da yake zantawa da manema labarai kan halin tsaro a yankin.

A cewarsa, an samu gagarumin ci gaba a bangaren tsaro sakamakon ƙoƙarin jami’an tsaro na gwamnati da na sa-kai, waɗanda ke bakin ƙoƙarinsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Alhamdulillahi, a yanzu muna cikin yanayi mai kyau na tsaro. Jami’an tsaro suna aiki tuƙuru, kuma hakan ya sa mutane ke gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, ingancin tsaron ya kai matsayin da ko mutum ya manta da kayansa a kasuwa, zai dawo ya same su ba tare da an taɓa su ba, lamarin da ya nuna yadda zaman lafiya ya wanzu a yankin.

Sarkin kasuwar ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa godiyarsa ga hukumomin tsaro na jihar Kaduna, bisa irin ƙoƙarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya a Fambeguwa da kewaye.

Haka kuma ya ja hankalin matasa da sauran al’umma da su guji shiga ƙungiyoyin banza ko aikata miyagun ayyuka, yana mai cewa hakan na da matuƙar muhimmanci wajen kare mutuncin kansu da na yankinsu.

Ya kuma shawarci matasa da su mayar da hankali wajen neman ilimin zamani da kuma koyon sana’o’in dogaro da kai domin inganta rayuwarsu da ta al’umma baki ɗaya.

A wani ɓangare, ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Sanata Uba Sani da ta tabbatar da rabon takin zamani ga manoma a kan lokaci, musamman ganin yadda damina ke ƙaratowa.

A cewarsa, idan aka tallafa wa manoma da kayan noma a kan lokaci, za su iya samar da wadataccen abinci ba kawai ga jihar Kaduna ba har ma da sauran jihohi.

A ƙarshe, Alhaji Nura Usman Oska ya taya Mai Martaba Alhaji Musa Alasan Baban Cukuri murnar ƙarin darajar sarauta da aka yi masa daga dagaci zuwa hakimi, tare da yi masa fatan alheri da samun nasara a sabuwar rawar da zai taka.

Ya kuma yi addu’ar zaman lafiya da ci gaba ga Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi