Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙungiyar kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) reshen Jihar Ogun ta yi kira mai ƙarfi ga hukumomi da su tabbatar an yi adalci kan zargin cin zarafin wata yarinya mai shekaru 11 a garin Mowe, tana mai gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na rufe shari’ar ba zai samu karɓuwa ba.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Afrilu, 2026, lokacin da yarinyar ke dawowa daga makarantar Islamiyya a kan titin Peace Lane, inda ake zargin wani mutum mai suna Michael ya tare ta tare da kai ta wani gini da ba a kammala ba.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar a jihar, Ustaadh Tajudeen Jimoh Alao, da sakatarenta, Ambasada Olaleye Rasheed Damilare, suka sanya wa hannu, MURIC ta bayyana lamarin a matsayin “laifi mai tsanani da aka tsara,” tana mai cewa wanda ake zargi ya kai harin ne cikin niyya.
ƙungiyar ta kuma bayyana damuwa kan rahotannin da ke nuna cewa wasu masu tasiri sun ziyarci iyalan yarinyar domin lallashinsu su janye ƙrar daga kotu su sasanta a waje. A cewar MURIC, irin wannan mataki na iya tauye adalci tare da ƙarfafa masu aikata irin wannan laifi.
“Abin takaici ne yadda ake ƙoƙarin nuna kamar adalci abu ne da ake iya saye da kuɗi. Wannan ba za mu lamunta ba,” inji ƙungiyar, wadda ta jaddada cewa kare wanda ake zargi da irin wannan laifi ya saɓa wa ɗabi’ar ɗan Adam.
Ta ƙara da cewa yarinyar na fuskantar mummunar illa ta ɓangaren tunani da zuciya, tana mai cewa irin wannan rauni na iya dawwama har tsawon rayuwa idan ba a yi adalci cikin lokaci ba.
MURIC ta yaba da yadda rundunar ’yan sanda ta yankin Mowe ta gudanar da bincike kan lamarin, musamman yadda aka miƙa shari’ar zuwa sashen kula da laifukan cin zarafi na jinsi a hedikwatar yankin ’yan sanda da ke Oke Ilewo a Abeokuta.
ƙungiyar ta kuma buƙaci al’umma, musamman mata da ’yan mata, da su riƙa bayyana irin waɗannan laifuka, tana mai jaddada cewa yin shiru na taimakawa masu laifi su ci gaba da aikata ta’asa ba tare da hukunci ba.
Haka zalika, ta yi kira ga gwamnatin Jihar Ogun da ta kafa kotuna na musamman domin sauraron shari’o’in fyaɗe da cin zarafin yara, tana mai cewa tsarin da ake da shi a yanzu na barin wasu masu laifi su tsere daga hukunci, yayin da waɗanda aka zalunta ke rayuwa cikin tsoro.
ƙungiyar ta kammala da jaddada cewa dole ne wanda ake zargi ya fuskanci cikakken hukuncin doka, tare da kira ga al’umma da su kasance masu lura amma cikin natsuwa, domin tabbatar da cewa adalci ya tabbata.
