Shugabannin kasuwannin kayan gwari a Kaduna sun koka da ɓullar tsutsar sharon

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Shugabannin kasuwannin kayan gwari a Jihar Kaduna sun bayyana damuwa kan yadda wata sabuwar tsutsa da ake kira “Sharon” ke ci gaba da lalata amfanin gonaki, lamarin da ke jefa manoma cikin asara mai tsanani.

Rahotanni sun nuna cewa matsalolin da ke addabar manoman kayan miya ba sabon abu ba ne, sai dai zuwan wannan tsutsa ya ƙara dagula al’amura fiye da yadda aka saba gani a baya. 

Shugabannin kasuwannin da ke yankunan ƙananan Hukumomin Kubau da Soba sun bayyana cewa duk da ƙoƙarin da ake yi na magance kwari, wannan tsutsa ta fi ƙarfin hanyoyin da aka saba amfani da su.

Alhaji Isma’ila Ahmed Soba, wanda shi ne mataimakin shugaban kasuwar ’yan gwari ta ƙaramar Hukumar Soba, ya bayyana cewa tun da dadewa ana fama da kwari masu lalata tumatir da sauran kayan miya.

Ya ce, duk da yawan irin waɗannan kwari, ana samun sauki idan ana yin feshin magungunan kwari akai-akai.

Sai dai ya jaddada cewa zuwan tsutsar “Sharon” ya sauya komai.

A cewarsa, manoma sun yi ƙoƙarin neman maganin wannan matsala amma har yanzu ba su samu nasara ba. “Lamarin ya yi tsanani matuƙa, domin mun yi iya bakin ƙoƙarinmu wajen nemo mafita amma abin ya ci tura,” inji shi.

Saboda haka, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani da ta tallafa musu wajen samar da maganin wannan tsutsa daga ƙasashen da suka ci gaba a fannin noman tumatir da sauran kayan miya. 

Haka kuma ya nemi gwamnati ta inganta samar da wutar lantarki a kasuwannin kayan gwari domin saukaka harkokin kasuwanci.

A nasa ɓangaren, Alhaji Gambo Dutsen Wai, shugaban kasuwar ’yan gwari ta Dutsen Wai a ƙaramar Hukumar Kubau, ya bayyana irin wannan damuwa, inda ya ce tsutsar “Sharon” na jefa manoma cikin asarar maƙudan kuɗaɗe a kowace shekara.

Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta ɗauki matakin gaggawa wajen kawo karshen wannan matsala da ke addabar manoma. Haka kuma ya roki Shugaban ƙaramar Hukumar Kubau, Alhaji Sale Banki, da ya yi la’akari da irin gudunmawar da kasuwar ke bayarwa ta fuskar haraji, tare da samar da muhimman ayyukan ci gaba kamar yadda ake yi a sauran kasuwanni a faɗin jihar.

Daga ƙarshe, ya yaba da ƙoƙarin shugabannin ƙananan hukumomi wajen bunƙasa yankunansu, tare da yi wa Jihar Kaduna da Nijeriya baki ɗaya addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa da ci gaba mai amfani.

By ukarofi