Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kano (KIRS), ta sanar da cewa ta samu sama da Naira biliyan 102 a matsayin kuɗin shiga na cikin gida (IGR) a shekarar 2025, adadin da ya nuna gagarumin ƙarin kuɗi idan aka kwatanta da Naira biliyan 74 da aka tara a shekarar 2024.
Shugaban hukumar, Zaid Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin bikin karramawa na shekarar 2026 da aka gudanar a birnin Kano a ranar Asabar, inda ya bayyana nasarar a matsayin wadda ba a taɓa gani ba a tarihin hukumar.
A cewarsa, wannan nasara ta samo asali ne daga ci gaba da aiwatar da gyare-gyare, inganta biyayya daga masu biyan haraji, da kuma ƙara ingancin ayyukan gudanarwa.
Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar hukumomi daban-daban na gwamnati ya taka muhimmiyar rawa wajen cimma wannan nasara.
“Gyare-gyaren da ake yi dole ne su haifar da sakamako a zahiri, kuma mun ga hakan ya tabbata,” inji Abubakar, yana mai cewa tsarin gudanar da haraji na hukumar ya samu babban cigaba cikin ‘yan shekarun nan.
Ya kuma jaddada muhimmancin sauya fasaha, inda ya ce sabbin manhajoji sun taimaka wajen ƙarfafa hulɗa da masu biyan haraji tare da sa ido kan yadda ake bin ƙa’idoji yadda ya kamata.
Shugaban ya kuma sake tabbatar da ƙudurin hukumar na kaiwa ga burin tara Naira biliyan 200 a nan gaba, yana mai kira ga ma’aikata da masu ruwa da tsaki su ci gaba da rike wannan gudu.
Abubakar ya yaba wa masu biyan haraji, ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati (MDAs), da sauran abokan hulda bisa goyon bayan da suke bayarwa, yana mai jaddada cewa haɗin kai na da matukar muhimmanci wajen dorewar wannan ci gaba.
A yayin taron, an karrama fitattun ma’aikata da wadanda suka bayar da gudunmawa ta musamman bisa ƙoƙarinsu. Shugaban ya ce an shirya wannan karramawa ne domin ƙarfafa kwazo da zaburar da ma’aikata su ƙara himma a aikinsu.
Tun da farko, Daraktar Sashen Kula da Albarkatun Dan Adam, Fatima Nuhu, wadda ta jagoranci kwamitin karramawar, ta bayyana cewa an gudanar da zabin cikin gaskiya da adalci, bisa cancanta. Ta kara da cewa an zaɓo waɗanda suka cancanta daga sassa daban-daban tare da bin ƙa’idoji masu tsauri domin tabbatar da gaskiya.
Ta kuma bayyana cewa kwamitin ya gudanar da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma ayyukan jin kai na kamfanoni (CSR) domin ƙarfafa amincewar jama’a da kuma wayar da kai kan muhimmancin biyan haraji.
A ƙarshe, ta yabawa ma’aikata da masu biyan haraji bisa gudunmawar da suka bayar, tana mai cewa wannan hadin kai ne ya zama ginshiƙin wannan gagarumar nasara da aka samu.
