Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da wani tallafi na sana’o’i da kayan more rayuwa da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 1.58, wanda Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua mai wakiltar Katsina ta Tsakiya ya samar domin inganta rayuwar al’umma.
An gudanar da ƙaddamarwar a filin wasa na Muhammadu Dikko dake cikin birnin katsina ,inda aka raba kayayyaki iri-iri da za su taimaka wajen ƙarfafa sana’o’i da rage zaman kashe wando a tsakanin jama’a.
Daga cikin kayayyakin da aka rabawa al’umma akwai motoci 40 da aka miƙa ma shugabannin jam’iyya, ƙungiyoyin addinai da wasu masu ruwa da tsaki, tare da motocin asibiti guda biyar domin tallafa wa harkokin kiwon lafiya.
Haka kuma, an raba tsabar kuɗi har Naira miliyan 150 ga jama’a.
Shirin ya kuma haɗa da rabon babura 410, injinan markaɗe 400, kekunan ɗinki 400 da kuma firij 200, baya ga babura masu ƙafa uku, domin taimaka wa mata da matasa su samu hanyoyin dogaro da kai da bunƙasa harkokin kasuwanci.
A fannin ilimi kuwa, an tallafa wa ɗaliban ƙaramar hukumar Ɗanmusa da kekunan hawa guda 100, domin sauƙaƙa musu zirga-zirga zuwa makarantu.
Da yake jawabi, Sanata Abdul’aziz Yar’adua ya bayyana cewa wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarinsa na inganta jin daɗin al’umma da ƙarfafa dogaro da kai.
A cewar sanatan wannan tallafi na kayan sana’a zai taka muhimmiyar rawa wajen rage rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasa. Yana mai cewa idan aka yi amfani da kayan yadda ya kamata, zai haifar da ƙarin ayyukan yi, ƙara kuɗaɗen shiga ga iyalai, tare da taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar baki ɗaya.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Dakta Bishir Gambo Saulawa, ya yaba da wannan shiri, yana mai jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin shugabanni wajen samar da ci gaba mai ɗorewa.
A nasa jawabin, Gwamna Raɗɗa ya jinjinawa Sanata Yar’adua bisa wannan gagarumin tallafi, tare da kira ga waɗanda suka amfana da su yi amfani da kayayyakin yadda ya dace, domin inganta tattalin arzikinsu da kuma rage talauci a faɗin jihar.
Gwamnan Dikko Raɗɗa sai ya jaddada buƙatar ci gaba da irin wannan shiri tare da sa ido domin tabbatar da cewa tallafin ya kai ga waɗanda suka fi buƙata.
