Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar Lajnatul Hisbah ta ƙasa reshen Jihar Katsina ta buƙaci al’umma musamman waɗanda suka cancanta su kaɗa ƙuri’a, da su gaggauta yin rijistar zaɓe domin mallakar Katin zaɓe na dindindin (PVC) gabanin babban zaɓen shekarar 2027, don zaɓen wakilai nagari.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai da ta gudanar a babban ofishinta da ke Masallacin Kandahar, Ƙofar Ƙaura, cikin birnin Katsina.
Babban kwamandan ƙungiyar na jihar, Malam Bilyaminu Muhammad Balalarabe, wanda ya jagoranci taron, ya ce lokaci ya yi da jama’a za su fahimci muhimmancin shiga harkokin zaɓe domin tabbatar da shugabanci nagari.
Ya ce hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sahihin zaɓe, amma nasarar kowanne zaɓe tana dogara ne da yadda jama’a suka bayar da cikakken haɗin kai.
Malam Bilyaminu ya ce rijistar masu zaɓe ginshiƙi ce ta dimokuraɗiyya, domin tana bai wa waɗanda suka kai shekaru 18 da kuma waɗanda ba su yi rijista a baya ba damar shiga cikin tsarin zaɓe.
Ya yi kira ga al’ummar Jihar Katsina da ma Najeriya baki ɗaya da suka cancanta su yi anfani da damar yin rijista domin mallakar PVC, wanda shi ne kaɗai ke ba mutum damar kaɗa kuri’a.
Malam Balarabe ya kuma jaddada buƙatar zaɓen shugabanni masu gaskiya, amana da ƙwarewa a zaɓen shekarar 2027.
A cewarsa, shugabanci nagari ne ke haifar da ci gaba, zaman lafiya da haɗin kai, don haka ya kamata masu zaɓe su yi la’akari da tarihin ’yan takara, kishin ƙasa da hangen nesa maimakon bambancin ƙabila, addini ko cin hanci.
Haka kuma, ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su fito da ’yan takara nagari tare da gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana da gaskiya.
Sannan ya buƙaci ƙungiyoyin farar hula, malamai, matasa da kafafen yaɗa labarai su bada tasu gudunmawa wajen wayar da kan jama’a da tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaɓe.
