Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Jinjina ga da jami’an tsaro da su ka yi kukan kura zuwa muguwar tungar ’yan ta’addan IP0B a jihar Imo inda hakan ya kai ga gano kabarin da a ke kyautata zaton nan ne a ka binne sojojin nan biyu Warrant Office Linus Audu da Private Gloria Mathew wadanda mugayen irin su ka kashe a shekara ta 2022 lokacin da su ke kan hanyar zuwa ɗaura musu aure a al’adance.
A lokacin kisan, mugayen ’yan IP0B da ’yan bindiga daɗinsu ESN sun kashe sojojin da yin gunduwa-gunduwa da sassan jikinsu, kuma har da naɗar ta’addancin a faifan bidiyo kamar dai yadda yaransu ’yan ta’addan daji ke yi in sun zo aikata muguwar manufarsu; yayin da ‘yan kan zaginsu na sohiyal midiya kan yi wuf su yi ta yayatawa kamar angulaye na yawo kan mushen jakin daji.
Tuni an tura kasusuwan zuwa ɗakin binciken asalin halitta DNA don tantancewa da kuma tuntuɓar danginsu don samun yi mu su jana’iza ta girmamawa. Kun tuna yadda ‘yan bazata su ka yi wa Janar Alkali kisan gilla a jihar Filato da ingiza motarsa cikin kududdufi inda su ka turbuɗe gawarsa a wulaƙantaccen rami. Wasu tsoffin mata kuma da ya dace su riƙa tsawatawa ‘ya’yansu, sai su ka yi gangami wai lallai ba za a yi binciken ba!.
Laifin Gloria wacce ‘yan jihar Imo ce shi ne, baya ga kasancewa jami’ar sojan Nijeriya, ta amince da auren Linus Audu da ya fito daga yankin kudancin Kaduna. An samu fa lokacin da wata ƙungiya a kudancin Kaduna ke cewa za ta haɗe da Biyafara in sun balle daga Nijeriya. Illar ruruta fitinar ƙabilanci kenan da mu ke magana inda wasu mutane kan zama tamkar dabbobi wajen yin gayawa jini na wuce ga mutane ‘yan uwansu don ƙiyayyar ƙabilanci.
ƙaryar Igbo zalla, Hausa zalla da kowane zalla na ƙabilanci, barazana ne ga zaman lafiyar ƙasa. Ya zama mai muhimmanci a cafke duk ‘yan zalla a wurga su gidan yari don ɗanɗana kuɗar muguwar zuciyarsu da daƙile kwangilar da su ke yi wa maƙiya Nijeriya da zaman salama.
Hatta wannan batu na awaren Biyafara ai masu jan zaren na neman mannawa ‘yan ƙabilar Igbo ne haƙƙin tsara komai da kuma zama a matsayin waɗanda za su ci gajiyar ƙasar Biyafara in an samu nasarar kafata. Abun mamaki sai ya zama ‘yan awaren na wannan zamani sun kafa sashen ‘yan bindiga wato ESN da kan yi dirar mikiya kan duk wanda tsautsayi ya fada kansa hatta su kansu Igbo. In har Igbo ba za su tsira daga kisan ESN ba ai ba ribar badi ba rai. Wannan na nuna ko an kafa Biyafara to wasu ne ‘yan kalilan za su bayyana daga wata uwa duniya su zama shugabannin kasar. Ko Nnamdi Kanu da ke zama madugu ai ya na da izinin zama ɗan Buraniya kuma can ma ya ke da zama fiye da jiharsa Abia. Ko kamo shi da a ka yi daga Kenya don fuskantar tuhumar cin amanar ƙasa da arcewa bayan samun beli, ai daga Burtaniya ya taho. Da dai bai fito daga Burtaniya ba, har yau da ya na nan da rediyonsa ya na ruruta fitinar kashe-kashe da muzgunawa jama’ar kudu maso gabar. Muƙarrabinsa ma Simon Ekpa ai mazaunin ƙasar Finland ne kuma a can a ka yi ma sa shari’ar da ta yi sanadiyyar wurga shi gidan yari.
Masu biyewa ‘yan IPOB a Arewa ko zama ‘yan kanzaginsu kan yi has ashen su na isar da saƙon da ke girgiza Lardin. Haba saƙon alheri ma yaushe ya isa wajen mutanen da a ke buƙata balle na gaggan matsorata da ko a yanar gizo ma ba sa iya bayyana kansu don kar a gano alaƙarsu da Gujjo KEFERO. Ina ma sakon ya ke ne, baya ga murde wuyan tarihi, zanen karya na manhajar AI da wankin FILTER sai in an shiga runtsi ba amsa a zunduma ashar. Ina ilimi a mai surfa ashar ko zabga karya?.
Tabbas ko sarautar da su ke murɗe tarihi cewa wasu sun kwace, a ka juya zamanin ya koma na sarakunan da su ke batu, to matsayinsu bai kai na yankawa dawaki ciyawa ba. Baubawan burmi gayyar soɗi karya ludayi ki biya kwano ai ba shi ma da darajar ba da tarihin sarauta don shi kansa ba da sahihin tarihi sai an haɗa da magada tarihin da su ma masu sarautar ne.
Ba buƙatar yaudarar kai, don gara mu shaidawa Bazatawa gaskiya duk da dama gaggan sun san gaskiyar amma ‘yan abi Yarima a sha kida ba lallai su gane kawai surutai ne na farafaganda kan yanar gizo, kuma ba ko Bahaushe daya Musulmi mai mutunci da ke wannan tafiyar. Mutanen nan dama su na nan tun daga kan kakanninsu zuwa iyaye har yaran na yanzu an gadar mu su wannan kiyayya ta musulmi da Musulunci. Duk wanda ka ga ya na rubutu kan tafiyar to dama rashin samun dama ta bulus ce ta soshiyal midiya ya sa ba ka ji amonsa ba. Babu abun da ya hada ikirarin mugun kamfen ɗin ba batun ɓarayin daji.
Ko gidadawa da a kan dau hotonsu wai sun yi taron ƙungiya ba su san ma me su ke ciki ba fiye da masu amfani da hotunan don farafagnda ko bunƙasa awalajar kwangila. Ba abun da ya haɗa Bahaushe ko Hausawa da wannan aiki na ‘yan bazata. Hasalima ‘yan bazata su ne makiya Hausawa lamba 1.
Batun wani sako na isa duk kurari ne kawai. Ba yadda za a yi mutum ya na rufe ruff a wayar salula cikin firgici da zullumi wai ya rubuta saƙo ya na isa!.
Na sha ganin ‘yan bazata na cewa ai Fulani sun kafa ƙungiyoyin Miyetti Allah waye-waye mai ya sa ba a hana su ba; sai da Hausawa su ka ce za su kafa ƙungiya ne a ke sukarsu. A nan kafin na yi nisa zan ce ba wanda a ka hana kafa ƙungiya sai dai kandagarki ga murde manufar kungiya zuwa ƙabilanci. Duk masu surutun wai Hausawa sun farka, yaudara ce kawai su ke yi don Hausawa dama a farke su ke tun fil azal kuma su ke mulkin kansu a dukkan matakai.
Kazalika waɗannan mutane masu iƙirarin Hausa zalla ba Hausawa ba ne. In kuma sun musa su fito fili daga firgici da tsoron sharrin kansu da su ke lulluɓe a ciki ta buɗe shafukan karya, ba hoton gaskiya ba sunan kwarai sai dogara ga manhajar Chatgpt da FILTER su na fito da hotunan wasu mutane kamar Larabawan Sudan masu rawuna da sunan wai tarihi su ke rubutawa. Kowa ya fito da siffar da Allah ya halicce shi kuma in ba munafurci, su bayyana kamar yadda mu ke a san su, ba ma sai wani ya yi zolaya wai a rantse da Alkur’ani ba. Wanda bai yi imani da Alkur’ani ba, mai ya sa zai damu da rantsuwa da Alkur’ani?.
Ga abubuwa 5 da na ke son jan hankali kan Makiyaya da Mahauta ko Makiyaya da Manoma:
1. Miyetti Allah da dangoginta na da rejista da CAC don kare muradun makiyaya amma sam ba Fulani ba. Shin Fulani nawa ne ke da rejista da ƙungiyar Miyetti? Fulani nawa ke da shanu? Ko kashi 1% na Fulani ba su da rejista da ƙungiyoyin makiyaya kuma hakkan ƙungiyoyin ba iya Fulani ba ne shugabanninsu har da wasu ƙabilu daban-daban, wanda ke da ja ya halarci taron Miyetti ya ga shugabannin ƙungiyar ya kuma ji shin ƙabilanci su ke tattaunawa ko batun kare muradun makiyaya? A gefe guda akwai ƙungiyoyin Mahauta da ke hulɗar kasuwanci kai tsaye da makiyaya kuma ba maganar kabilanci a Mahauta sai sarrafa nama don masu son shan romo a ƙasar nan su samu su sha lagwadarsu har ma waɗanda ba sa barin fatar shanu komai sai sun lashe.
2. A gefen manoma akwai ɗimbin ƙungiyoyin gama-kai na manoma wadanda su ma abokan huldar makiyayan ne. A ɓangaren manoma akwai kowace ƙabila har su kansu Fulani da ke da mafi rinjaye a makiyaya. Rikici tsakanin manoma da makiyaya ba sabon abu ba ne kuma kowa ya san ba abun da ya hada wannan da ƙabilanci.
3. Akwai wata kungiyar Fulani makiyaya FUDECO da duk ayyukanta sun shafi koyar da sana’a ne ga makiyaya waje da harkar kiwo kaɗai. Duk mai son bincikawa ko ta manhajar AI zai iya dubawa zai gani. Sai wata Tabital Fulaku da ke da muradun dawo da al’adun kawaici na Fulani daga sauye-sauye zamani masu ruguza tarbiyya.
4. A duk garuruwan da ke waje da kokuwar Arewa akwai sarakunan Hausawa da na wasu manyan ƙabilu na Nijeriya. Duk mai son bincikawa zai iya yin hakan hatta a ƙasar Yarbawa da yankin Igbo. Manufofin wadannan sarakuna ba ƙabilanci ba ne sam sai don zama dandalin tattaunawa da kare kyawawan al’adu da ƙarfafa ‘yan uwantaka da addini.
5. A Binuwai TIV da Makiyaya ko Fulani abokan wasa ne amma sai da ‘yan siyasa su ka cusa muradunsu na son kai wajen wargaza wannan zama na makiyaya da MUN CI wato TIV da ke cinye shanun Fulani. Tsohon gwamnan Binuwai Samuel Otom na daga waɗanda su ka yi mulki da fakewa da ƙabilanci. Ba ma sai na shiga jihar Filato ba inda ya dace masu iƙirarin ‘yan ƙasa ne su zauna lafiya da makiyaya amma sai abun ya juye kiyayya inda har wasu ke zuba guba shanu su ci su mutu, su kuma ‘yan bulus su kwashe mushe su gasa su kora goskolo.
Ba wata ƙungiya ko daya da ke da rejista a Nijeriya kan ƙabilanci hatta wannan ƙungiya mai cewa wai an koyawa Hausawa ƙabilanci ne, ba wanda ya ma ta rejista da sunan HAUSA ZALLA.
KAMMALAWA
Ba wani ko wasu al’umma da ba za su iya kafa ƙungiya musamman ta sana’ar da su ka fi kwarewa a kai kamar manoma, maƙera, masunta, majema, masaka, maɗinka, Fatake da sauransu. In ka ga mutum ya shigo da ƙabilanci to tabbas ya ɗauko kwangila daga logar IPOB ne masu son wargaza ƙasa.
