Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar Kotun Jihar Adamawa da ke zamanta a Yola ta soke tarukan gangamin Jam’iyyar ADC da aka gudanar a jihar ranar Litinin.
A hukuncin da Mai Shari’a Isah Ahmed ya yanke, ya bayyana cewa taron bai inganta ba saboda karya ƙa’idojin da aka shimfiɗa. Kotun ta ce taron ya saɓa wa Sashe na 84(4) na Dokar Zaɓe da kuma Sashe na 18 na kundin tsarin mulkin ADC, don haka ya zama haramtacce.
Alƙalin ya ƙara da cewa waɗanda ake tuhuma sun yi watsi da ƙa’idojin da aka tanada, suka rungumi abin da ya kira “ƙa’idojin da suka ƙirƙira da kansu.”
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Shugaban ADC na Jihar Adamawa, Kwamred Shehu Yohanna ya shigar, inda ya ƙalubalanci taron bisa rashin bin doka da tsarin jam’iyya.
Da yake mayar da martani, tsohon sakataren yaɗa labarai na ADC, Honarabul Martins Dickson, ya ce jam’iyyar ta karɓi hukuncin kotu da hannu biyu, tana kuma jiran umarnin shugabancin jam’iyyar na ƙasa a Abuja kan matakin da za a ɗauka.
Dickson ya bayyana cewa hukuncin ya shafi taron gangamin jam’iyyar, wanda ke nufin dukkan shugabannin da aka zaɓa ta wannan hanya ba za su ci gaba da aiki ba a halin yanzu.
Sai dai ya ƙara da cewa Dokar Zaɓe ta cire duk wani cikas ga ayyukan jam’iyyar, inda mambobin jam’iyya za su iya ba da izini ga kowane ɗan jam’iyya ya gudanar da wasu ayyuka na jam’iyyar har ma da na shugabanci idan buƙata ta taso.
Ya yi kira ga mambobi da magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar da cewa shugabannin jihar sun riga sun tuntuɓi shugabannin jam’iyyar na ƙasa don ɗaukar matakin da ya dace.
Dickson ya kuma bukaci jama’a da su yi watsi da iƙirarin Kwamred Shehu Yohanna wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban ADC a Jihar bayan hukuncin, yana mai jaddada cewa hukuncin mai shari’a Isah Ahmed ya sake tabbatar da hukuncin da mai shari’a Manji na Babbar Kotun Yola ta yanke a baya, wanda ya tsige Yohanna daga shugabancin ADC a jihar.
