Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bayanan da Hukumar Kula da Bashin ƙasa ta Nijeriya (DMO) ta fitar sun nuna cewa, jihohi 32 da Babban Birnin Tarayya Abuja sun ƙara tara kusan dala biliyan 1 na sabon bashi na waje a shekarar 2025, duk da ƙarin kuɗaɗen da suke samu daga Asusun Rabon Kuɗin Tarayya (FAAC).
Rahoton da jaridar News Point Nigeria ta samu ya nuna cewa jimillar bashin waje na jihohi 36 da Abuja ya tashi daga dala biliyan 4.80 a ƙarshen Disamba 2024 zuwa dala biliyan 5.68 a ƙarshen Disamba 2025. Wannan na nufin ƙarin dala miliyan 884.66, wanda ya kai kashi 18.43 cikin ɗari a cikin shekara guda.
Bincike ya nuna cewa jihohi 33 daga cikin 37 sun ƙara bashinsu, yayin da kaɗan kaɗan suka rage. Wannan yana nuna yadda yawancin gwamnatocin jihohi ke ci gaba da dogaro da rance na ƙasashen waje, duk da yawan kuɗin shiga da suke samu daga FAAC sakamakon hauhawar farashin mai, canjin darajar naira da kuma cire tallafin man fetur.
Rahoton ya ƙara bayyana cewa jimillar ƙarin bashi da aka ɗauka ya kai dala miliyan 944.12, yayin da raguwar bashin da wasu jihohi huɗu suka yi ya kai dala miliyan 59.46 kacal. Wannan ya sa jimillar ta ƙaru da dala miliyan 884.66 baki ɗaya.
Idan aka sauya wannan adadi da kuɗin musayar shekarar 2025 da DMO ta yi amfani da shi (N1,435.2571 kan dala 1), wannan ƙarin bashin yana kaiwa kusan tiriliyan N1.36.
Daga cikin jihohin da suka rage bashin akwai Jihar Edo, Ribas, Anambra da Bayelsa. Jihar Edo ce ta fi ragewa da dala miliyan 29.02, yayin da Ribas ta rage dala miliyan 28.69. Anambra ta rage kaɗan da dala miliyan 1.11, sannan Bayelsa ta rage da dala miliyan 0.64.
Sai dai duk da wannan ƙananan raguwar, yawancin jihohi sun ƙara bashi sosai. Katsina ta ninka bashinta kusan sau biyu, Kaduna ta ƙara dala miliyan 59.19, yayin da Kogi ta ƙaru da sama da kashi 126 cikin ɗari. Haka kuma Neja da Filato sun samu ƙaruwa mai tsanani, inda Plateau ta fi kowa ƙaruwa da kusan kashi 187 cikin ɗari.
Gombe ma ta fito fili da ƙaruwa mai yawa, inda bashinta ya tashi daga dala miliyan 33 zuwa dala miliyan 88.66, wato ƙaruwa da kashi 168.70 cikin ɗari. Imo kuwa ta ƙara dala miliyan 45.64, yayin da Oyo ta ƙara dala miliyan 34.71.
A gefe guda kuma, Legos – wadda ita ce ke da mafi yawan bashi na waje a Nijeriya – ta samu ƙananan ƙaruwa ne kawai, duk da cewa bashinta ya kai dala biliyan 1.17.
Binciken ya nuna cewa yawancin kuɗaɗen da jihohi ke rancewa suna fitowa ne daga cibiyoyin bada rance na duniya (multilateral institutions), yayin da rance daga ƙasashen biyu ko bankunan kasuwanci ya yi ƙasa.
Wannan yanayi na ƙaruwa da bashi na zuwa ne duk da rahoton da ya nuna cewa FAAC ya ƙaru da sama da Naira tiriliyan 2 a shekarar 2025, wanda ke nuna cewa maimakon rage dogaro da bashi, yawancin jihohi suna ci gaba da faɗaɗa shi.
Masana da kuma masu bibiyar tattalin arziki sun nuna damuwa kan wannan yanayi, suna mai gargaɗin cewa idan ba a sauya hanya ba, hakan na iya shafar ci gaban ayyukan gwamnati da kuma ɗorewar tattalin arziki a matakin jihohi.
