Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Farashin man fetur ya ɗan ragu a ranar Litinin, 4 ga Mayu, 2026, bayan Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasar Amurka za ta fara wani shiri na taimaka wa jiragen ruwa da suka maƙale a Mashigin Hormuz.
Rahotanni sun nuna cewa farashin man Brent ya ragu da kashi 0.1 cikin ɗari, inda ya sauka da centi 6 zuwa dala 108.11 kan kowace ganga a lokacin 0400 GMT, bayan ya riga ya ragu da dala 2.23 a ranar Juma’a.
Shi kuwa man West Teɗas Intermediate (WTI) na Amurka ya tsaya a dala 101.50 kan kowace ganga, bayan ya ragu da centi 44, wato kashi 0.4 cikin ɗari, bayan asarar dala 3.13 a ranar Juma’a.
Trump ya ce, a ranar Lahadi cewa Amurka za ta fara jagorantar jiragen ruwa domin su fita lafiya daga Mashigin Hormuz, amma duk da hakan farashin mai ya ci gaba da kasancewa sama da dala 100 kan kowace ganga, saboda babu wata yarjejeniyar zaman lafiya a gani, sannan jigilar kaya ta wannan muhimmiyar hanya ta ruwa ta ci gaba da fuskantar takura.
Tattaunawa tsakanin Amurka da Iran ta ci gaba a ƙarshen mako, inda ɓangarorin biyu ke nazarin martanin juna kan batutuwan da ke tsakaninsu.
Shugaban Amurka Donald Trump na ganin cimma yarjejeniyar nukiliya da Tehran a matsayin muhimmin abu, sai dai Iran na son a dakatar da tattaunawar nukiliya har sai bayan ƙarshen rikici, tare da buƙatar a fara cire takunkumin da ke kan jigilar kaya a yankin Gulf.
Wata mai sharhi daga kamfanin Phillip Noɓa, Priyanka Sachdeɓa, ta bayyana cewa kasuwar mai na ci gaba da samun goyon baya saboda matsalolin samar da mai da kuma rikicin siyasa da ke ci gaba da tasiri.
Ta ce, muddin ba a samu tabbataccen sulhu da zai dawo da jigilar mai yadda ya kamata a Mashigin Hormuz ba, farashin mai zai ci gaba da kasancewa sama, tare da yiwuwar ƙarin tashin farashi a gaba.
A gefe guda kuma, ƙungiyar ƙasashe Masu Fitar da Man Fetur da kawayenta, wato OPEC+, ta sanar da cewa za ta ƙara yawan man da ake samarwa da ganga 188,000 a kowace rana a watan Yuni ga ƙasashe bakwai, wanda hakan shi ne karo na uku a jere na ƙarin samarwa.
Rahoton ya nuna cewa wannan ƙari ya yi daidai da wanda aka amince da shi a watan Mayu, sai dai ban da kaso na Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), wadda ta fice daga OPEC a ranar 1 ga Mayu, kamar yadda kamfanin Reuters ya ruwaito.
Duk da haka, ana sa ran wannan ƙarin samarwa zai kasance ne a rubuce kawai muddin rikicin Iran da sauran ƙasashen yankin ya ci gaba da tarwatsa jigilar man fetur ta Mashigin Hormuz.
