Yaƙin Iran ya lanƙawame wa Amurka kusan Dala biliyan 29 – Pentagon

Spread the love

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar a ranar Talata cewa kuɗin da Amurka ta kashe kan yaƙin Iran ya kai kusan Dala biliyan 29, bisa sabon ƙiyasin da aka fitar yayin zaman sauraron kasafin kuɗi a Majalisar Dokokin ƙasar.

Sabon adadin ya fi wanda sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya bayar kimanin makonni biyu da suka gabata da dala biliyan huɗu.

Pete Hegseth tare da Janar Dan Kaine sun bayyana haka ne yayin da suke kare buƙatar kasafin kuɗin tsaro ta shekarar 2027 da ta kai dala tiriliyan 1.5, inda aka tambaye su kan kuɗin da aka kashe a yaƙin Iran.

Jules Hurst, shugaban sashen kuɗi na Pentagon wanda shi ma ya halarci zaman, ya ce a ranar 29 ga Afrilu, an kiyasta kuɗin da aka kashe kan yaƙin da dala biliyan 25.

Sai dai ya ce tawagar hafsoshin soji da masu binciken kuɗi na ci gaba da sa ido kan sabon ƙiyasin, kamar yadda BBCHausa ta ruwaito.

By Babaji