Atiku ya buƙaci gwamnati ta kawo ƙarshen tsare El-Rufa’i

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da ta jihar Kaduna da su gaggauta sako tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i.

Atiku ya ce, cigaba da tsare shi a daidai lokacin da Musulmi ke shirin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah ba dace ba, yana mai caccakar matakin tsare tsohon gwamnan.

Ya bayyana al’amarin a matsayin abin damuwa da ke barazana ga ‘yancin jama’a, mutuncin dimukraɗiyya da kuma bin doka da oda, inda ya zargi gwamnatin tarayya da amfani da ƙarfin gwamnati wajen tsoratar abokan hamayya a siyasa.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga Atiku akan hulda da jama’a, Phrank Shaibu ya fitar, inda ya bayyana cigaba da tsare El-Rufa’i a matsayin abin damuwa, mai tada hankali a fagen siyasa, kuma wanda bai dace da ka’idojin adalci, dimukraɗiyya da mutuntakar ɗan-adam ba.

Sanarwar ta ce, “Babbar Sallah lokaci ne na tausayi, sulhu da nuna dan Adamci. Babu wani dalili da zai sa a hana mutum kasancewa tare da iyalansa a irin wannan lokaci mai muhimmanci ga addini, musamman idan ba a nuna cikakken bin ka’idojin doka ba.

“Saboda haka, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar na kira da a gaggauta sakin Malam El-Rufai, sannan ya bukaci dukkan hukumomin da abin ya shafa da su guji siyasar gaba da juna, su yi abin da zai tabbatar da adalci, zaman lafiya da hadin kan kasa.”

By Babaji