Hajji 2026: Maniyyatan farko daga Kano sun tashi zuwa Saudiyya

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jirgin farko na alhazan jihar Kano ya tashi zuwa Saudi Arabia domin gudanar da ibadar hajjin bana.

Rukunin farko na alhazan 558 ya tashi ne a jirgin Max Air daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano zuwa birnin Madinah da misalin ƙarfe 12:48 na dare a yau Asabar, 16/05/2026.

Rahotanni sun nuna cewa alhazan sun isa Filin jirgin Madina da misalin ƙarfe 7:35 na safe.

A cikin maniyata 558 da suka tashi 333 maza ne sai mata 225.

Kazalika, alhazan da suka tafi sun fito ne daga ƙananan hukumomi Dala, Gwale Ungoggo da kuma Fagge.

By ukarofi