Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jamila Abdu Yandoma ta zama yar takarar kujerar majalisar wakilai da ke wakiltar ƙananan hukumomin Mani da Bindawa a Jihar Katsina bayan kammala zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a tsakaninta da Ahmed Sale da suka fito daga Mani.
Ita dai Jamila ta doke abokin hamayyar ta Ahmed Sale da kuri’a 24989′ shi Kuma ya Sami kuri’a 1056 Kamar yadda shugaban kwamitin zaɓe Shuaibu Duwan ya sanar a ɗakin taro na ƙaramar hukumar Mani.
A jawabin ta Jamila Abdu Mani tayi godiya ga gwamna Dikko Raɗɗa da yaba mata dama suka shiga majalisar zartarwa ta jiha da kuma wannnan dama da ta sami na takaran.
Hajiya Jamila ta kuma yi godiya ga ya’yan jamiyar a waɗannan ƙananan hukumomi da suka fito gaba ɗayan su suka zaɓe ta.
Yan takarar tayi alƙawarin idan Allah ya bata nasara ta ci zaɓe za ta mai da hankali wajen cigaban yankin musamman mata da yara yan gudun hijira da basu da matsuguni.
Jamila Abdu Mani idan har ta ci zaɓe za ta zama ta biyu bayan marigayiya Yaha Mani da ta taɓa zama wakiliya a majalisar wakilai ta ƙasa.
Sai dai abokin takaran ta Ahmed Sale bai halarci wurin zaɓen ba, kuma babu wani bani inda yake a lokacin.
