Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Aƙalla maniyyata uku daga jihar Jigawa da ke shirin gudanar da aikin Hajjin bana na 2026 a ƙasar Saudiyya sun rasa kuɗaɗe da wasu kayayyaki masu muhimmanci sakamakon satar da aka yi musu a biranen Makkah da Madinah.
ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, wani dattijo Bafulatani mai suna Baba Katanga daga ƙauyen Katanga da ke ƙaramar hukumar Kiyawa, ya bayyana cewa ya yi asarar dala Amurka 400 bayan hawa tasi daga Masallacin Harami zuwa otel ɗinsa mai suna Mahabbat Al Akhawin da ke Makkah.
Maniyyacin ya zargi direban motar da amfani da damar da ya samu yayin da yake duba katin Nusuk ɗinsa wajen sace kuɗin.
“Na yi matuƙar mamaki lokacin da na sake dubawa na gano dala 400 ɗina sun ɓace. Hankalina ya tashi domin wannan ne kuɗin da zan yi amfani da su tsawon zamana,” inji shi.
A wani makamancin lamarin kuma, wani maniyyaci Bafulatani daga ƙaramar hukumar Jahun ya rasa dukkan kuɗin dalolinsa bayan zargin wani direban tasi da aikata sata a irin wannan yanayi, sai dai ba a bayyana sunansa ba.
Haka kuma wata mahajjaciya da aka fi sani da Hajiya ta rasa jakarta da ke ɗauke da wayoyin hannu guda biyu da kuma kuɗaɗen da za ta riƙa kashewa yayin aikin Hajji. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a Miƙat da ke Madinah, wurin da maniyyata ke shiryawa domin gudanar da Umrah.
Majiyoyi sun bayyana cewa matar ta ɗan bar jakarta ba tare da kulawa ba kafin daga bisani ta gano cewa an sace ta.
Wannan lamari ya jefa mahajjatan Jigawa cikin damuwa, inda wasu daga cikinsu suka fara tara kuɗi domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa kafin samun wani tallafi daga hukumomi.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmad Umar Labbo, ya tabbatar da cewa hukumar za ta tallafa wa mahajjatan domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.
Ya kuma sake jaddada gargaɗin da hukumar ke yi wa mahajjata da su kasance masu taka-tsantsan tare da kauce wa barin kayayyaki masu muhimmanci babu kulawa ko kuma bai wa baƙi amanarsu, musamman a wuraren ibada masu cunkoso da tashoshin sufuri.
Labbo ya yi addu’ar Allah ya kare dukkan mahajjata tare da ba su nasarar kammala aikin Hajji lafiya.
