Daga tarihin karramawa zuwa sabuwar alƙiblar Nollywood: Cikakken nazari kan manyan nasarorin AMVCA 2026

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Da yammacin ranar Asabar ne titunan yankin Victoria Island da ke Jihar Iko suka fara cunkoso tun kafin a isa lokacin fara bikin karramawa mafi girma a masana’antar fina-finai ta Afirka, wato Africa Magic Viewers’ Choice Awards 2026. Motoci masu tsada suna jerawa a kofar Eko Hotel & Suites yayin da dubban masoya nishadi, ‘yan jarida, masu ɗaukar hoto da masu sharhi daga sassa daban-daban na duniya suka mamaye wajen domin shaida abin da mutane da dama suka kira “daren da zai tantance sabbin sarakunan Nollywood.”

Tun daga wajen jan kafet, ana iya fahimtar cewa AMVCA ta bana ba irin ta kowace shekara ba ce. Yanayin wajen ya cika da walwala, ɗaukar hoto, hasken fitilu masu walkiya da kuma gasa tsakanin taurari wajen nuna kayan alfarma mafi kayatarwa. Jarumai mata sun bayyana cikin dogayen kaya masu kyalli da aka tsara da salon Afirka na zamani, yayin da jarumai maza suka fito cikin shiga irin ta manyan taurarin Hollywood, abin da ya kara nuna yadda Nollywood ke ƙoƙarin kai kanta matakin duniya.

Sai dai duk wannan walwala ba ita ce kadai ta dauki hankalin jama’a ba. A cikin dakin taron, inda manyan taurarin Afirka suka hallara, ana ta rade-radin sunayen fina-finan da ake hasashen za su mamaye gasar. Sunaye irin su ‘My Father’s Shadow’, ‘Lisab’i: A Legend Is Born, ‘The Herd’ da ‘To Kill A Monkey’ sun mamaye tattaunawar da ake yi a tsakanin baki da masana harkar nishadi.

A shekarun baya an saba ganin fina-finai na barkwanci ko kuma manyan fina-finai na kasuwanci suna mamaye AMVCA. Amma a wannan shekara, ‘My Father’s Shadow’ ya zo da wani sabon salo da ya sa mutane da dama suka fara cewa Nollywood na shiga wani sabon zamani.

Lokacin da aka sanar da fim ɗin a matsayin wanda ya lashe Best Movie, dakin taron ya kaure da tafi da ihu. Wasu daga cikin masu aikin fim ɗin sun rungumi juna cikin farin ciki, yayin da wasu ke hawaye saboda tsananin farin cikin nasarar da suka samu bayan watanni da shekaru suna aiki tuƙuru.

Masu sharhi sun bayyana cewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka sa fim ɗin ya yi nasara shi ne yadda ya haɗa labari mai zurfi da fasahar ɗaukar hoto, sauti da kuma salon ba da labari irin wanda ake gani a manyan fina-finan duniya. Wasu ma sun ce wannan nasara wata alama ce da ke nuna cewa masu kallon Nollywood sun fara karkata zuwa fina-finai masu ma’ana da zurfin tunani.

Daraktan fim ɗin, Akinola Davies Jr., ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da suka fi ɗaukar hankali a daren bayan ya lashe kyautar Best Director. A jawabinsa bayan karɓar kyautar, ya yaba wa dukkan masu aikin fim ɗin tare da bayyana cewa, nasarar ba tasa kaɗai ba ce, nasara ce ta duk masu ƙoƙarin ɗaga martabar fina-finan Afirka.

Wani abin da ya ƙara jawo hankali shi ne yadda fim ɗin ya lashe kyaututtuka a ɓangarori masu muhimmanci kamar rubutu, sauti da kuma manyan fannoni na fasaha. Wannan ne ya sa masana da dama suka ce ‘My Father’s Shadow’ ba kawai fim ne mai daɗi ba, fim ne da aka gina cikin ƙwarewa da tsari irin na ƙasa da ƙasa.

Idan akwai wani abu da AMVCA 2026 ta sake tabbatarwa, to shi ne yadda fina-finan harshen gida suke ƙara samun matsayi a Nollywood.

Fim ɗin ‘Lisabi: A Legend Is Born’ ya zama ɗaya daga cikin fina-finan da aka fi magana a kansu tun kafin ranar bikin. Fim ɗin, wanda ya mayar da hankali kan tarihi da jarumtakar gargajiya, ya samu karɓuwa sosai daga masu kallo saboda yadda aka haɗa al’ada, tarihi da kuma ingantaccen ɗaukar hoto.

Lokacin da aka sanar da shi a matsayin wanda ya lashe Best Indigenous Language Film (West Africa), mutane da dama sun miƙe tsaye suna tafi. Wannan nasara ta ƙara ɗaga martabar jarumi kuma furodusa Lateef Adedimeji, wanda a cikin ‘yan shekarun nan ya zama ɗaya daga cikin fitattun masu shirya fina-finan tarihi a Nollywood.

Masana suna ganin cewa nasarar ‘Lisabi’ wani saƙo ne ga sauran masu shirya fina-finai cewa masu kallo suna ƙara sha’awar ganin labaran Afirka da suka shafi tarihi, al’adu da asalin rayuwa.

Wani mai sharhi a harkar fim ya bayyana cewa: “Yanzu mutane sun fara gajiya da labaran kwaikwayo iri ɗaya. Suna son su ga kansu, tarihinsu da al’adunsu a cikin fina-finai. Wannan shi ne dalilin da ya sa fina-finai irin ‘Lisabi’ suke samun karɓuwa sosai.”

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

By ukarofi