Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta yi gyara ga babbar dokar aikin duba gari ta ƙasa tare da sanya mata hannu domin bai wa malaman tsafta damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata da kuma gurfanar da masu karya dokokin tsafta a faɗin jihar.
Mataimakin babban jami’in da ke kula da sashen duba gari na malaman tsafta a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina, Sanitarian Kabir Ahmad ne ya bayyana hakan yayin wani gangamin masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Katsina.
Ya ce gyaran dokar wani muhimmin mataki ne na inganta lafiyar al’umma da kuma tabbatar da tsaftar muhalli a dukkan ƙananan hukumomin jihar.
A cewarsa, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya sanya hannu kan dokar domin ta fara aiki nan ba da jimawa ba, wanda hakan zai bai wa jami’an tsafta cikakken ƙarfi na doka wajen gudanar da aikinsu.
Sanitarian Kabir Ahmad ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta maido da aikin duba gari na malaman tsafta, inda jami’an tsafta za su rika zagayawa gida-gida domin tabbatar da cewa an kare iyalai daga kamuwa da cututtuka masu alaka da rashin tsaftar muhalli tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin tsafta da kula da muhalli.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su bayar da haɗin kai ga jami’an tsafta domin tabbatar da nasarar aiwatar da dokar da kuma samar da ingantaccen muhalli mai tsafta ga kowa.
