ADC ta naɗa tsofaffin gwamnoni a matsayin jagororin zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa

Spread the love

Jam’iyyar adawa ta ADC ta naɗa tsohon Gwamnan Jihar Cross River, Sanata Liyel Imoke, da tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, domin jagorantar kwamitocin zaɓen fidda gwani gabanin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da jam’iyyar za ta gudanar nan gaba.

Yayin da Sanata Imoke zai kasance Shugaban Kwamitin Tantance ’Yan Takarar Shugaban Ƙasa, Abdulfatah Ahmed zai jagoranci Kwamitin Zaɓen Shugaban Ƙasa, kamar yadda Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya bayyana.

Sauran mambobin Kwamitin Tantance ’Yan Takarar Shugaban Ƙasa sun haɗa da Hon. C.I.D. Maduabum a matsayin Sakatare, Alhaji Lawal Batagarawa, Farfesa Bode Ayorinde, Hon. Nnena Elendu-Ukeje, Farfesa David Salifu, da Kanal Abubakar Ali Ciroma.

Kwamitin Zaɓen Shugaban Ƙasa yana da Farfesa Yisa Gana a matsayin Sakatare, tare da Manjo Janar Adamu Jalingo, Dr. Auwalu Anwar, Chief Emenike Ikechi, Dr. Macaulay Iyare, Tajudeen Bakare, Dattijo Ubolo Itodo Okpanachi, Zainab Buba Galadima, Uzoamaka Onyeama, da Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris a matsayin mambobi.

Jam’iyyar ta kuma kafa Kwamitin Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa wanda Dr. Suleiman Usman, SAN, zai jagoranta, yayin da Barr. Ken Imasuagbon zai kasance Sakatare, sannan Barr. Dare Okerade zai kasance mamba.

Dangane da zaɓen fidda gwani na gwamna, ADC ta kafa kwamitocin tantancewa guda biyu. Kwamitin farko yana ƙarƙashin jagorancin S.E. Aruwa, SAN, tare da Femi Olawuyi, Esq a matsayin Sakatare. Sauran mambobin sun haɗa da Lauretta Onochie, Chief Dr. (Mrs.) Vivian E. Ugochukwu, Akilu Indabawa, Ibrahim Mohammed Wali, da Farfesa Rabiu Bello.

Kwamitin tantancewar gwamna na biyu yana ƙarƙashin jagorancin Barr. Justina Abanida, tare da Hon. Chille Igbawua a matsayin Sakatare. Sauran mambobin sun haɗa da H.E. Gerrard Irona, Sanata Yisa Braimoh, Hassan Mohammed Ibrahim, Joseph Ephraim Enemali, da Kyaftin Aliyu Ngolmo na Rundunar Ruwa.

Jam’iyyar ta kuma amince da kwamitocin ɗaukaka ƙara na zaɓen gwamna guda biyu. Kwamitin farko yana ƙarƙashin jagorancin P.I. Oyewole Esq, tare da Abdulhakeen Taiye Ibrahim a matsayin Sakatare da Adah Usman a matsayin mamba. Kwamitin ɗaukaka ƙara na biyu kuwa yana ƙarƙashin jagorancin M.E. Sheriff, Esq, tare da Barr. Realwan Okpanachi a matsayin Sakatare da Barr. Hassan Yakubu a matsayin mamba.

ADC ta bayyana cewa an tsara kwamitocin cikin tsanaki domin tabbatar da gaskiya, amana, adalci, da dimokuraɗiyya ta cikin gida a dukkan matakan gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

By Babaji