
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohuwar Ministar Jin-ƙai da Harkokin Ci-gaban Al’umma, Sadiya Farouq ba ta da isasshen lafiya inda a yanzu take ƙasar Misra domin karɓar magani, kamar yadda lauyanta, Oladipo Okpesheyi ya bayyana.
Rahotanni sun bayyana cewa, Sadiya Farouk tare da Bashir Nura Alƙali, wanda shi ne Babban Sakataren ma’aikatar da wani Sani Mohammed, ana tuhumar su ne da hannu a laifuka guda 12 masu alaƙa da cin amana da wulaƙanta ofis da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta maka su a kotu akansu.
EFCC ta yi zargin cewa tsohuwar ministar da sauran waɗanda ake tuhumar su tare sun sauya akalar kusan Dala miliyan 1.3, wato kimamin Naira miliyan 746 a lokacin da take jagorantar ma’aikatar.
An gabatar da tuhume-tuhumen ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a unguwar Apo.
A watan Afrilu ne kotun bada izinin kama Sadiya Farouk da Alƙali, lamarin da ya sa EFCC ta sanar da neman tsohuwar ministar ruwa-a-jallo bisa zargin wulaƙanta aiki da sauya akalar dukiyar al’umma.
A yayin sauraron shari’ar a ranar Litinin, lauyan da ke kare ɓangaren EFCC, Rotimi Jacobs (SAN), ya shaida wa kotun cewa an shirya gurfanar da al’amarin amma kuma Sadiya Farouk ba ta samu zuwa ba ba tare da wani bayani ba.
Akan haka ne lauyan ɓangare su Sadiya, Okpesheyi ya tabbatar wa kotun cewa zai kawo tsohuwar ministar acikin wata guda domin tabbatar da hukunci akan al’amarin.
