NDC ta ƙara wa’adin sayen fom ɗin shiga takara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar adawa ta NDC, ta sanar da ƙara wa’adin sayen fom ɗin neman tsaya wa takara ga masu ra’ayin shiga a matakan majalisun dokokin ƙasa da na jihohi da kuma na takarar gwamna.

A wata sanarwa da Sakatarenta na Ƙasa, Ikenna Morgan Enekweizu ya fitar a ranar Talata, ya ce jam’iyyar ta sanar da Lahadi, 17 ga watan Mayu, 2026 da misalin ƙarfe 6 na yamma a matsayin lokacin da za ta rufe sayarwa.

A cewarsa, a yanzu an ƙara tsawon wa’adin zuwa ƙarfe 12 na daren ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu, 2026 a matsayin lokacin da za ta rufe sayar da fom ɗin shiga takara.

Haka kuma, jam’iyyar ta ce za a fara tantance ‘yan takarar da suka sayi fom a ranar Talata, 19 ga Mayu, 2026 har zuwa ranar 26 ga watan, wato tsawon mako guda kenan.

Sakataren ya ƙara da cewa, za a yi aikin karɓa da dawo da fom daga ‘yan takarar da aka tantance daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Mayu, 2026.

NDC ta kuma bayyana cewa, ba za ta sake ƙara wani wa’adi ba akan wanda ta bayar a yanzu, tana mai kira ga dukkan masu sha’awar shiga takara da su hoɓɓasa wajen ganin sun cika dukkan sharuɗɗan da ta tanada.

By Babaji