
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanata Barau I. Jibrin ya sake zama ɗan takarar sanatan mazaɓar Kano Ta Arewa a Majalisar Dattawa ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC a zaɓen 2027, da ke tafe.
Wannan shi ne karo na huɗu da sanatan ke zama ɗan takarar kujerar a ƙarƙashin jam’iyyar.
Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Maifata ne ya bayyana haka a ofishinsa jim kadan bayan kammalla taron kaddamar da takarar Danmajalisar dattawan kasar nan a garin na Bichi, a yayin da yake tattaunawa da Jami’ar Yada Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo.
Alhaji Hamza Sule Maifata, ya kuma ce, gagarumin taron an gudanar da shi a cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da tada kayar baya ba, bisa yadda yankin suka amince ya sake wakiltarsu a zabe na gaba, duba da irin dimbun ayyukan alheri da ya dukufa da yi domin cigaban al’umma.
“Wakilcin da mai girma Sanata yake yi a wannan yanki namu da jiha da ma kasa baki daya; kowa ya san irin ayyukan da suke yi na alheri, sun gina al’umma kuma suna yin ayyukan raya kasa da duk abin da ya dace, kuma dama shi mutum yana yin zabe ne domin a wakilce shi, a kuma yi masa wakilci na gari ta kowane fanni kuma ba ta inda Barau ya gaza , sai dai a yi musu fatan alheri.” Alhaji Hamza Sule Maifata.
Kazalika, ya bayyana taron ya samu halartar Mataimakin Gwamna, Alhaji Murtala Suke Garo da ya je a madadin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf domin ganin yadda za a gudanar da zaben.
Har’ila yau a cikin jawabinsa, daga cikin mahalarta taron akwai; shi Kansa dantakarar Sanata Barau I Jibril da ‘yan Majalisar Tarayya da Jihohi na da na yanzu da Shugabannin Jam’iyyar APC na Kano Ta Arewa.
A wani bangare na labarin daga cikin mahalarta taron, Malam Hassan Abdu Bichi, ya yi matukar godiya ga Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a bisa halin jinkai da hidimta wa al’umma da ya sa a gaba.






