
Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana a gaban kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC domin neman tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Atiku na daga cikin manyan masu neman tikitin jam’iyyar tare da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da kuma ɗan kasuwa Mohammed Hayatudeen.
A ranar Laraba ne Atiku ya isa otal ɗin Transport Hilton da ke Abuja domin tantancewar, tare da rakiyar wasu manyan jiga-jigan siyasa da suka haɗa da tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami; tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal; tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha; da kuma tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Maina Waziri.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce ya gabatar wa kwamitin tsarin farfaɗo da tattalin arziki da kuma shirin magance matsalar tsaro da ke addabar ƙasar.
Ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki, rashin aikin yi, rushewar kasuwanci da kuma ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane.
Atiku ya ce shirinsa zai mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa zuba jari, daidaita tattalin arziki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomin tsaro.
Ya ƙara da cewa, Nijeriya na buƙatar shugabanci mai ƙwarewa da hangen nesa domin ceto ƙasar daga matsalolin da take ciki na tsawon lokaci.
