Kamfani ya ba al’umma haƙuri kan kuskuren fim ɗin Wata Shida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kamfanin Al-Hayat International ya nemi afuwar al’umma musamman Hausawa akan wani kuskure da aka yi yayin ɗaukar shirin fim ɗin WATA SHIDA, yana mai neman da a yafe masa akan haka.

A wani gajeren saƙo da Shugaban kamfanin, Baba Hayatu ya fitar a ranar Laraba, Al-hayat International ya ce al’amarin ya faru ne bisa ajizancin ɗan-adam.

Akan haka ne shugaban ya ce, suka ɗauki matakin gyara domin kauce wa sake faɗa wa irin kuren baya ga halin tashin hankali da suka tsinci kansu aciki a kai.

A cewarsa, tuni suka duƙufa wajen neman gafarar Allah da yin alƙawarin hakan zai sake faruwa ba.

“..muna ta ƙoƙarin gyarawa a gaba don kada haka ya sake faruwa, kuma muna ta tuba ga ALLAH dan wallahi wannan ba ƙaramin kuskure ba ne”, inji shugaban.

Haka kuma, cikin alhini da nuna baƙin akan faruwar al’amarin, Baba Hayatu ya ƙara da cewa, “…ina Mai godiya ga kowa da kowa da ya nuna ɓacin ransa da ganin wannan mummunar kalla wa’iyazubillah, kuma ya yi ƙoƙarin jawo hankalinmu akan mu gyara.”

A ƙarshe, a madadin kamfanin, ma’aikatansa da masana’antar Kannywood, ya ce suna jaddada ba wa al’umma haƙurin faruwar al’amarin da fatan Allah ya yafe musu.

By Babaji