Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta zargin cewa yana yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu aiki a ɓoye domin tazarcensa a zaɓen 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Global Tɓ, inda ya ce mutane marasa hankali ne kawai za su yarda da irin wannan zargi.
Ya ce shi da magoya bayansa suna aiki ne kawai domin jam’iyyar NDC, ba domin wata jam’iyya ko dan takara ba.
Ya ƙara da cewa duk da cewa Tinubu babban abokinsa ne tun shekaru da dama, hakan ba yana nufin za su haɗa aƙidunsu na siyasa ba.
Kwankwaso ya kuma zargi makusantan shugaban ƙasa da ɓoye masa haƙiƙanin matsalolin da ƙasar ke fuskanta, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun fi mayar da hankali wajen jan gwamnoni zuwa APC.
Game da haɗakarsa da Peter Obi a jam’iyyar NDC, Kwankwaso ya ce sun zabi goyon bayan Obi ne bayan nazari da suka yi, inda suka ga shi ne mafi dacewa daga yankin kudancin Nijeriya.
Ya kuma bayyana cewa haɗakar tasu na da isasshen lokaci kafin zaben 2027 domin jawo hankalin ‘yan Nijeriya da kuma bayyana gaskiya kan raɗe-raɗin da ake yaɗawa.
