Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mai Bai Wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu Shawara Na Musamman Kan Yaɗa Manufofi da Sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi a sassan ƙasar nan duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta.
Bwala ya ce, Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya bai wa ’yan ƙasa damar kare kansu idan aka kai musu hari, musamman idan rayuwarsu na cikin haɗari.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Laraba, yayin da yake tsokaci kan hare-haren da suka faru a aauyen Esiele da ke ƙaramar Hukumar Orire a Jihar Oyo.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ’yan bindiga sun kai hari makarantu a yankin, inda suka sace malamai da ɗalibai.
Da yake mayar da martani, Bwala ya ce ko da gwamnati ta yi iya bakin ƙoƙarinta, akwai mugayen mutane da ke aikata laifuka a ko ina cikin duniya.
“A matsayinmu na al’umma, za mu kawo ƙarshen wannan matsala. Duk lokacin da aka rasa rayukan ’yan Nijeriya, dole ne mutane su nuna damuwa da alhini,” inji shi.
Ya kuma yi zargin cewa rikice-rikicen tsaro kan ƙaru ne a lokutan da ake daf da zaɓe, yana mai cewa wasu na anfani da abin domin cimma muradunsu na siyasa da tattalin arziki.
“A duk lokacin da zaɓe ya gabato tun daga shekarun 2014, 2018, 2022 har zuwa yanzu a 2026, ana ganin rikice-rikice na ƙaruwa saboda wasu na anfani da abin a matsayin wata hanyar kasuwanci da anfani,” ya ce.
Bwala ya jaddada cewa kundin tsarin mulki ya amince da kare kai idan mutum ya fuskanci barazana.
“Idan wani ya shiga gidana domin kashe ni, duk wata hanya da zan bi wajen kare kaina kundin tsarin mulki ya amince da ita,” inji shi.
Sai dai ya bayyana cewa ba kowane irin makami ne doka ta bai wa fararen hula damar mallaka ba, yana mai cewa dole ne a bi tsarin doka wajen neman izinin wasu nau’ikan makamai.
Haka kuma ya yabawa ƙungiyoyin sa-kai da masu bayar da bayanan sirri a wasu jihohi, musamman a Borno, inda ya ce suna taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙi da ta’addanci.
Bwala ya ƙara da cewa haɗin kan jama’a da hukumomin tsaro tare da bayar da sahihan bayanai ne zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Nijeriya.
