Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Yankin Neja Delta (NDPHC) ya bayyana shirinsa na ƙara megawatt 1,500 na wutar lantarki zuwa cibiyar samar da wuta ta Jihar Legas domin rage matsalar ƙarancin wutar lantarki da jihar ke fama da ita.
Babbar Darakta kuma Shugabar Kamfanin NDPHC, Jennifer Adighije, ce ta bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da ta kai wa Babbar Daraktar Hukumar Kula da Tsarin Wutar Lantarki ta Jihar Legas (LASERC), Temitope George.
A cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na kamfanin, Emmanuel Ojor, ya fitar, Adighije ta ce NDPHC na da kusan megawatt 2,000 na ƙarfin samar da wutar lantarki da ba a amfani da shi yadda ya kamata, wanda za a iya amfani da shi domin inganta samar da wuta a Legas sosai.
Ta bayyana cewa duk da cewa ana buƙatar kusan megawatt 12,000 a Legas, jihar na samun kusan megawatt 1,000 ne kawai daga babbar tashar rarraba wutar lantarki ta ƙasa, lamarin da ke nuna gibin wutar lantarki mai yawa.
Adighije ta ce kamfanin NDPHC na aiki a dukkan sassan harkar wutar lantarki, tun daga samar da iskar gas, samar da wuta, jigilar wuta da kuma rarrabawa, wanda hakan ke ba shi damar taka muhimmiyar rawa wajen rage matsalar ƙarancin wuta.
Ta ƙara da cewa kamfanin na da ƙarfin samar da kusan megawatt 4,000, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƙarfin samar da wuta a yankin Afirka ta kudu da hamadar Sahara, amma a yanzu yana iya aika tsakanin megawatt 400 zuwa 500 ne kawai a kullum saboda matsalolin kayayyakin more rayuwa da kuma ƙalubalen kasuwa.
“Wannan na nuna cewa akwai ɗimbin ƙarfin samar da wuta da ba a amfani da shi wanda za a iya amfani da shi domin ƙara samar da lantarki,” inji ta.
Shugabar ta kuma yi nuni da rahoton kasuwar wutar lantarki ta Legas wanda ya bayyana cewa akwai babban giɓi a ɓangaren samar da makamashi a jihar, tana mai cewa NDPHC a shirye take ta haca gwiwa da LASERC domin faɗaɗa samar da wutar lantarki ga jama’a.
Ta bayyana Legas a matsayin babbar kasuwar wutar lantarki mai armashi, tana mai cewa kamfanin a shirye yake ya zuba jari mai yawa a ɓangaren jigilar wuta da rarrabawa domin tabbatar da ingantacciyar wuta mai sauƙin samu da araha.
A nata martanin, Babbar Daraktar LASERC, Temitope George, ta yi maraba da wannan haɗin gwiwa tare da jaddada aniyar gwamnatin Jihar Legas na inganta samar da wutar lantarki.
Ta yabawa gudunmawar da NDPHC ke bayarwa a fannin wutar lantarki, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa haɗin gwiwar zai taimaka wajen samar da daidaitacciyar wuta a faɗin jihar.
George ta kuma tunatar da shirin hukumar na samar da wutar lantarki na sa’o’i 24 a wasu yankunan jihar, tana mai cewa ƙarin ƙarfin wuta da zuba jari a kayayyakin more rayuwa daga NDPHC zai taimaka wajen cimma wannan buri cikin sauri.
