
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanata mai wakiltar mazaɓar Oyo ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sharafadeen Alli, ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Oyo, bayan da ya doke manyan abokan hamayyarsa a zaɓen da aka gudanar.
Rahotanni sun bayyana cewa Alli ya samu ƙuri’u 578,143, wanda hakan ya ba shi nasarar zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar.
Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya zo na biyu da ƙuri’u 19,193, yayin da wani ɗan takara guda ɗaya ma ya shiga takarar.
Nasarar ta Sharafadeen Alli na zuwa ne yayin da jam’iyyar APC ke cigaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen gwamna a jihar Oyo.
