Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masana harkokin lafiya sun bayyana cewa sama da kashi 80 cikin 100 na mazaje a Nijeriya masu fama da cutar kansar mafitsara na zuwa asibiti ne a makare, lamarin da ke sanya cutar ta yi tsanani har ta kai ga wahalar warkarwa.
Sun danganta hakan da tsoro, shiru da kuma rashin ingantaccen bayani game da cutar.
Daraktan Asibitin The Prostate Clinic (TPC), Farfesa Kingsley Ekwueme, ya bayyana haka a Legas, inda ya ce manufarsu ita ce rage yawan masu zuwa da cutar ta kai matakin ƙarshe a Nijeriya.
Ya ce, bayan shekaru da ya kwashe yana aiki a ƙasar Birtaniya, inda gano cutar da wuri da kuma amfani da hanyoyin magani na zamani suka taimaka wajen ceton rayuka, ya ga dacewar zuba jari a ɓangaren lafiya a Nijeriya.
A cewarsa, sankarar mafitsara na daga cikin manyan cututtukan da ke kashe maza a Nijeriya saboda yawancin marasa lafiya na zuwa asibiti ne bayan cutar ta tsananta, lokacin da hanyoyin magani suka ragu.
Sai dai ya ce, a Birtaniya ana gano mafi yawan masu cutar tun tana matakin farko, wanda hakan ke sauƙaƙa maganinta.
“Bambancin sakamakon yana da girma ƙwarai,” inji shi, yana mai jaddada cewa gano cutar da wuri da fara magani cikin lokaci na da muhimmanci wajen ceton rayuwa.
Farfesa Ekwueme, wanda ƙwararren likitan tiyatar mutum-mutumi ne (Robotic Surgeon), ya ce idan aka gano sankarar prostate da wuri tana da magani, kuma marasa lafiya na iya ci gaba da rayuwa kamar yadda aka saba.
Ya bayyana cewa asibitinsu ya yi wa marasa lafiya daga Nijeriya da wasu ƙasashe tiyata, inda ya ce mutane na zuwa Legas domin samun magani sannan su koma ƙasashensu cikin ƙanƙanin lokaci bayan an yi musu tiyata.
Likitan ya kuma sanar da gina cibiyar tiyatar mutum-mutumi a jihar Imo, wadda za a saka na’urar tiyatar Da ɓinci — daya daga cikin manyan na’urorin tiyata na zamani a duniya.
Ya ce, cibiyar za ta kasance daidai da ƙa’idojin ƙasashen duniya, kuma za a kammala ta nan ba da jimawa ba.
Haka kuma ya bayyana shirin kafa wata “birnin lafiya” da za ta haɗa ayyukan tiyatar mutum-mutumi da kuma kula da masu fama da cutar daji a wuri guda domin bai wa marasa lafiya cikakken kulawa.
A cewarsa, ƙwararru daga Birtaniya na taimaka musu wajen tsara aikin, kuma ana son cibiyar ta zama babbar cibiyar kula da masu fama da cutar daji a Afirka.
Farfesa Ekwueme ya ƙara da cewa suna horas da ma’aikatan lafiya ’yan Nijeriya yadda za su sarrafa na’urorin zamani domin rage dogaro da ƙwararrun ƙasashen waje.
Da yake magana kan abubuwan da ke haddasa cutar, ya ce shekaru, asalinsu da kuma tarihin iyali na daga cikin manyan abubuwan haɗari.
Ya ce maza baƙar fata na cikin waɗanda ke fuskantar hatsarin kamuwa da nau’in cutar mai tsanani, musamman idan sun fara tsufa.
Ya kuma yi gargaɗi kan yarda da bayanan da ba su da tushe daga kafafen sada zumunta dangane da hanyoyin kariya daga cutar, yana mai cewa babu wata hujjar kimiyya da ta tabbatar da wani abinci ko salon rayuwa da zai hana kamuwa da sankarar prostate.
Likitan ya shawarci jama’a da su riƙa yin gwaji akai-akai maimakon dogaro da jita-jita.
A ɓangaren magani kuwa, ya soki tsofaffin hanyoyin cire mazantaka kai tsaye ga masu fama da cutar, yana mai cewa a yanzu magunguna da dabarun zamani sun fi dacewa wajen kula da marasa lafiya tare da kare musu ingancin rayuwa.
Ya kuma bayyana cewa nasarar tiyata na da alaƙa da ƙwarewar likitan da ke gudanar da ita, yana mai kwatanta aikin tiyata da harkar jiragen sama da ke buƙatar horo da bin ƙa’idojin tsaro sosai.
Daga cikin waɗanda suka ba da shaidar yadda suka warke akwai tsohon Kakakin Rundunar Sojin Nijeriya, Manjo Janar John Enenche (mai ritaya).
Ya ce, wani irin gargaci ne ya sa ya je ya gwada lafiyarsa bayan ya fara lura da wasu sauye-sauye a jikinsa.
“An gano alamar cutar a jikina, sai tsoro ya kama ni. Na ce wa likita ya cire komai domin kawai na rayu,” in ji Enenche.
Sai dai ya ce Farfesa Ekwueme ya ba shi kwarin gwiwa tare da amfani da hanyar magani ta zamani, inda aka yi masa tiyatar mutum-mutumi cikin nasara.
“Na shiga asibiti da ƙafafuna, kuma na fita da ƙafafuna. Kuɗin da na kashe bai kai darajar rayuwar da na samu ba,” inji shi.
Sauran marasa lafiyar da suka ba da labarinsu sun haɗa da Emmanuel Okolie daga Canada, wanda ya ce ya bar tsarin jinkirin magani a ƙasar Canada ya dawo Nijeriya domin samun kulawa.
