Daga UMAR GARBA a Katsina
Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta yi kira ga iyaye da ɗaukacin al’umma da su ƙara sanya ido sosai kan tarbiyyar yara, musamman matasa maza da mata, yayin shagulgulan bukukuwan Sallah domin kare su daga faɗawa munanan ɗabi’u da ka iya lalata tarbiyya da zaman lafiyar al’umma.
Bayanin haka na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, wadda jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, AA Bazariye ya sanya wa hannu aka rabawa manema labarai a Katsina.
Sanarwar ta bayyana cewa lokutan bukukuwan Sallah na daga cikin lokutan da wasu ke amfani da damar wajen jawo matasa zuwa ayyukan da ba su dace ba, ciki har da shaye-shaye, sata, yawo barkatai, rashin kula da lokutan dawowa gida da sauran ɗabi’u da suka saɓawa koyarwar addinin Musulunci da kyawawan al’adun Hausawa.
Hukumar ta buƙaci iyaye da masu kula da tarbiyya da su kasance masu lura da irin wuraren da ‘ya’yansu ke zuwa, abokan hulɗarsu da kuma yadda suke gudanar da lokutansu musamman daga ranar Sallah, daren Sallah har zuwa bayan Sallah.
Har ila yau, hukumar ta jaddada muhimmancin sanya tufafin da suka dace da tarbiyya da mutunci tare da kaucewa sanya matsatsun kaya da duk wani salo ko ɗabi’a da zai iya jawo fitina ko karya dokokin addini.
Hukumar ta kuma yi kira ga ɗaukacin al’umma da su taimaka wajen sanya ido kan masu shigo da miyagun ƙwayoyi cikin unguwanni domin sayarwa ga matasa, tana mai bayyana cewa amfani da miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan musabbabin tashin hankali, aikata laifuffuka, sare-sare da asarar rayuka a cikin al’umma.
Sanarwar ta ƙara da cewa haɗin kai tsakanin jama’a, jami’an tsaro da hukumar Hisbah na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Don haka, hukumar ta buƙaci jama’a da su riƙa bayar da sahihan bayanai da goyon baya domin daƙile duk wani abu da zai kawo barazana ga tsaro da tarbiyya.
Hukumar ta tabbatar da cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga tsaro, tarbiyya da zaman lafiyar al’umma ba, tare da ɗaukar matakan da suka dace bisa tanadin doka domin kare jama’a.
A karshe, Hukumar ta yi addu’ar Allah (SWT) ya tabbatar da zaman lafiya, Ya kare matasa daga munanan ɗabi’u, ya kuma albarkaci Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.
