
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji ya zama ɗan takarar gwamnan a Jihar Inugu a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP a zaɓen 2027 da ke tafe.
Rahotanni sun bayyana cewa, Nnaji ya yi nasarar haka ne bayan samun ƙuri’a 7,424, lamarin da ya ba shi damar doke Mista Samson Nnamani, wanda ya samu ƙuri’a 600 a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar a ranar Litinin.
Da yake jawabi jim-kaɗan bayan sanar da shi a matsayin wanda ya yi nasara, Nnaji ya bayyana godiyarsa ga mambobin jam’iyyar bisa amincewa da shi wajen ba shi damar tsaya wa takarar, yana mai tabbatar musu da cewa zai yi amfani da ita yadda ya dace.
A baya ne dai jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta tilasta masa yin murabus daga muƙamin minista akan zarge-zargen yana amfani da shaidar kammala karatu ta bogi.
