Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar Katsina ta kawo asarar shaguna 10 tare da asarar ɗimbin dukiya.
Ana zargin inverter mai amfani da hasken rana da haddasa gobara a babbar kasuwar Katsina
Rahotanni sun bayyana cewar gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 6:35 na safiya, inda hukumar kashe gobara ta jihar Katsina ta ce ta samu kiran gaggawa kafin jami’anta su isa wurin domin shawo kan lamarin.
A cewar hukumar, gobarar ta shafi shaguna 10 da suka haɗa da na kayan masarufi, abubuwan sha, labule da yadudduka. Sai dai jami’an kashe gobara sun samu nasarar ceto wasu shaguna bakwai tare da hana wutar bazuwa zuwa wasu sassa na kasuwar.
Haka kuma ta ce an ceci shaguna masu lamba 112 zuwa 114 da dukiyoyin da ke cikinsu, ciki har da mota kirar Peugeot 406, amma shaguna masu lamba 128 zuwa 130 sun ƙone gaba ɗaya amma ba a rasa rai ko ɗaya ba a cewar hukumar.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa gobarar na iya samo asali ne daga matsalar lantarki da ta shafi inverter mai amfani da hasken rana, yayin da hukumomi ke ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin gobarar.
