
Yayin da cece-kuce ke cigaba da mamaye zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, shugabannin jam’iyyar sun buƙaci Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen da su nemi hakkinsu ta hanyoyin doka maimakon fito-na-fito a kafafen yaɗa labarai.
Kakakin ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa har yanzu babu wata hujja da ke tabbatar da cewa an tafka maguɗi ko murɗe sakamakon zaɓen domin fifita tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV, inda ya ce ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen daga jihohin ƙasar nan, don haka bai kamata a yi gaggawar yanke hukunci ba.
Rahotanni sun nuna cewa Atiku Abubakar na kan gaba a sakamakon farko-farko da aka samu, yayin da Rotimi Amaechi ke matsayi na biyu, sai Mohammed Hayatu-Deen a matsayi na uku.
Sai dai Amaechi da Hayatu-Deen sun yi watsi da sakamakon, suna zargin cewa an hana mambobin jam’iyyar da dama damar kaɗa ƙuri’a tare da yin maguɗi wajen gudanar da zaɓen.
Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar na da hanyoyin warware koke-koke, yana mai tabbatar da cewa INEC ta sanya ido a dukkan matakan gudanar da zaɓukan fidda gwani na jam’iyyar a jihohi 36 da Abuja.
Ya kuma ce jam’iyyar ba ta damu da wata ɓangarenta da ta ayyana Dumebi Kachikwu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ba, domin a cewarsa, INEC ta san sahihin shugabancin ADC da ke karkashin jagorancin David Mark.
