Kotu ta umarci a mayar da tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman kurkukun Kuje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotu ta bayar da umarnin a mayar da tsohon Ministan Wutar Lantarki na Najeriya, Saleh Mamman, zuwa gidan gyaran hali na Kuje domin fara zaman hukuncin da aka yanke masa na shekaru 75 a gidan yari.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan samun sa da laifukan almundahana da karkatar da kuɗaɗen gwamnati yayin da yake riƙe da muƙaminsa a gwamnatin tarayya.

Hukuncin ya biyo bayan shari’a mai ɗaukar lokaci inda aka gabatar da hujjoji da dama kan yadda aka zarge shi da hannu wajen karkatar da biliyoyin naira.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan kammala shari’ar, jami’an tsaro sun karɓe shi daga harabar kotun domin aiwatar da umarnin mayar da shi gidan yarin Kuje da ke Abuja, yayin da ake sa ran lauyoyinsa za su iya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ta yanke.

By Babaji