Babbar Sallah: Gwamna Raɗɗa ya yi kira da a yi addu’o’in zaman lafiya ga ƙasa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya aike da gaisuwar Sallar Layya ta Eid-el-Adha ga ɗaukacin musulmi a Jihar Katsina, a faɗin Najeriya da kira ga al’ummar musulmi da su cigaba da yiwa ƙasa addu’a samun zaman lafiya.

Ya bayyana wannan biki a matsayin babban abin tunatarwa kan ɗabi’un imani, biyayya, da sadaukarwa ba tare da neman wani abu a madadinsa ba. Ɗabi’u da ya dace kowane shugaba da kowane ɗan ƙasa su sanya a zuciyarsu.

Gwamnan ya jaddada cewa ranar arafah wadda ita ce tsakiyar aikin Hajji lokaci ne mai cike da albarka, inda Allah ke karɓar addu’o’in bayin sa da wata rahama ta musamman. Ya roƙi Musulmi a Katsina da sauran sassan duniya da su yi amfani da wannan dama mai tsarki su dage da addu’a domin samun zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali mai ɗorewa a jihar da kuma Najeriya.

Gwamna Raɗɗa ya kuma tuna da babban darasi da ke cikin miƙa wuya da Annabi Ibrahim A.S ya yi, yana mai cewa wannan darasi fitila ce ga shugabanni a lokacin ƙunci da jarabawa.

Ya yi wa dukkan alhazai da ke gudanar da aikin Hajji a yanzu fatan ibada mai karɓuwa da tafiya lafiya, yana addu’ar Allah ya karɓi ibadarsu, ya kuma mayar da su gida cikin ƙoshin lafiya tare da albarkar Hajji Mabrur.

Har ila yau, ya buƙaci Musulmi da su yi amfani da lokacin Sallah wajen ƙarfafa danƙon zumunci, da taimakon mabuƙata, da kuma yaɗa ɗabi’un tausayi da zaman lafiyar jama’a da suke cikin asalin koyarwar Musulunci.

Gwamnan ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta “Gina Gobenku” na tabbatar da walwala, tsaro, da cigaban dukkan mazauna Jihar Katsina ba tare da nuna banbancin addini ko ƙabila ba, ya kuma yi alƙawarin ci gaba da aiki ba dare ba rana domin hidimtawa al’umma.

By ukarofi