Matuƙar hukumomin tsaro suna iya gano ‘yan ƙasa da ‘yan mediya, za su iya gano waɗanda suka sace ɗaliban Oyo, inji Buratai

Spread the love

Tsohon Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya bayyana cewa hukumomin tsaro na Nijeriya na da cikakken ƙarfin gano tare da kamo masu garkuwa da mutanen da suka sace wasu ɗalibai da malamai a Jihar Oyo.

Buratai ya ce, bai yarda cewa masu laifin sun fi ƙarfin hukumomin tsaron ƙasar ba, yana mai jaddada cewa idan jami’an tsaro na iya gano wuraren da wasu ‘yan ƙasa ko masu tasiri a kafafen sada zumunta suke, to tabbas za su iya bin sawun masu garkuwa da mutane da kuma gano inda suke.

Tsohon hafsan sojin ya bayyana cewa ci gaban fasaha da hanyoyin tattara bayanan sirri da hukumomin tsaro ke da su a yau sun isa su taimaka wajen gano masu aikata irin waɗannan laifuka, musamman idan aka yi amfani da su yadda ya kamata.

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen amfani da dabarun leƙen asiri da fasahar zamani domin ceto waɗanda aka sace tare da tabbatar da an hukunta masu hannu a lamarin.

Kalaman Buratai na zuwa ne bayan rahotannin sace wasu ɗalibai da malamai a Jihar Oyo, lamarin da ya sake tayar da damuwa kan matsalar garkuwa da mutane da rashin tsaro a wasu sassan Najeriya.

Masu sa ido kan harkokin tsaro na ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da dakile ayyukan masu aikata laifuka.

By Babaji