Zargin zambar biliyan N2.8: Kotu ta jinkirta yanke hukunci kan buƙatar dakatar da shari’ar Hadi Sirika

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama, Abuja, ta jinkirta yanke hukunci kan bukatar da aka gabatar na dakatar da shari’ar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, da ake zargi da hannu a damfarar kwangiloli ta kusan Naira biliyan 2.83.

Mai shari’a S.C. Oriji ne ya bayyana hakan yayin zaman kotu ranar Talata, a shari’ar da Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta shigar kan Sirika, diyarsa Fatima Hadi Sirika, da surukinsa Hamma Jalal Sule.

EFCC na tuhumar wadanda ake kara da laifuka shida da suka shafi zargin bada kwangiloli ba bisa ka’ida ba ga kamfanin Al Buraƙ Global Investment Limited, wanda ake dangantawa da ɗiyarsa Fatima.

A yayin zaman kotun, lauyan wanda ake ƙara na uku, Sanusi Musa (SAN), ya buƙaci kotun ta hana masu gabatar da kara gabatar da karin hujjoji ko shaidu a shari’ar.

Haka kuma ya nemi kotun ta soke dukkan hujjoji da takardun da aka riga aka gabatar tare da yin watsi da karar baki ɗaya.

Sanusi Musa ya yi hujjar cewa an fara shari’ar ne tun kafin a kammala bincike yadda ya kamata, don haka bai kamata a ci gaba da ita ba.

Sai dai lauyan EFCC, Rotimi Jacobs (SAN), ya yi fatali da wannan bukata, yana mai cewa dokar Administration of Criminal Justice Act (ACJA) 2015 ta bai wa masu gabatar da kara damar gabatar da karin hujjoji ko shaidu a kowane mataki kafin a yanke hukunci na karshe.

Ya kuma ce akwai hukunce-hukuncen Kotun Koli da Kotun ɗaukaka ƙara da suka tabbatar da hakan.

Da yake yanke hukunci kan buƙatar, Mai Shari’a Oriji ya bayyana cewa duk da cewa wadanda ake ara suna da damar gabatar da korafe-korafe kafin a yanke hukunci, batutuwan da aka kawo suna da alaƙa kai tsaye da ainihin karar da ake yi.

Saboda haka, ya ce zai fi dacewa a yanke hukunci kan wannan buƙata tare da hukuncin ƙarshe na shari’ar gaba ɗaya.

Kotun ta ɗage zaman shari’ar zuwa 10 ga Yuni, 2026, domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Wannan na nufin cewa bukatar dakatar da shari’ar, soke hujjojin da aka gabatar da kuma yin watsi da tuhume-tuhumen za a yanke hukunci a kansu ne tare da hukuncin ƙarshe na shari’ar.

By ukarofi