’Yan majalisar wakilai shida daga Oyo sun fice daga PDP zuwa APM

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Aƙalla ‘yan majalisar wakilai shida daga jihar Oyo sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APM, a wani mataki da ake ganin yana ƙara nuna tasirin siyasar gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta wasiƙun sauya sheƙar ‘yan majalisar 13 a zaman majalisar na ranar Talata bayan hutun Sallah. ‘Yan majalisar Oyo da suka koma APM sun haɗa da Anthony Adebayo, Adedeji Olajide, Sunday Makanjuola, Oyedeji Oyeshina, Fola Oyekunle da Adigun Adekunle.

A wasiƙunsu, sun bayyana rikice-rikicen cikin gida da takaddamar shugabanci a PDP a matsayin dalilin ficewarsu. Hakan ya sa Makinde ya tafi da ‘yan majalisa shida daga cikin ‘yan majalisar wakilai 14 na jihar Oyo zuwa APM.

A gefe guda kuma, PDP ta rasa wasu mambobi amma ta samu sababbi a majalisar. Auwalu Gwalabe daga Bauchi ya koma APM daga PDP, yayin da Shehu Dalhatu daga Katsina ya fice daga APC zuwa PDP. Haka kuma, Etanabene Benedict daga Delta da Aleɗ Egbona sun koma PDP daga LP da APC bi da bi.

Sannan ɗan majalisar Edo, Esosa Iyawe, ya fice daga APC zuwa NDC, yayin da Gbefwi Gaza daga Nasarawa ya sauya sheƙa daga SDP zuwa LP. Wannan ci gaba na nuna yadda sauya sheƙar ‘yan siyasa ke ci gaba da girgiza fagen siyasar Nijeriya gabanin zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply