Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da ƙara wa’adin fara aiwatar da dokar da ta wajabta sanya tsarin tantance wurin aiki (Geo-Fencing) ga na’urorin biyan kuɗi na POS zuwa 1 ga Agusta, 2026.
Matakin, wanda bankin ya bayyana a wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 29 ga Mayu, 2026, na da nufin bai wa cibiyoyin kuɗi da masu samar da ayyukan biyan kuɗi ƙarin lokaci domin kammala shirye-shiryen da suka dace da sabon tsarin dokokin da aka shimfiɗa.
Sanarwar ta samu sa hannun Daraktar Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi na CBN, Dakta Rakiya Yusuf, kuma an aike ta zuwa ga Bankunan Kasuwanci, Bankunan ƙananan Kuɗaɗe, wato Microfinance Banks, masu gudanar da harkokin kuɗi ta waya, kamfanonin sarrafa hada-hadar kuɗi, masu samar da na’urorin PoS da sauran hukumomi da kamfanonin da ke da lasisin gudanar da ayyukan kuɗi a ƙasar.
A cewar CBN, an ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma la’akari da wasu ƙalubalen fasaha da na gudanarwa da suka taso daga umarnin da aka bayar tun a watan Agustan 2025 kan sauya tsarin bayanan biyan kuɗi zuwa ISO 20022 da kuma wajabta sanya tsarin gano wurin na’urorin biyan kuɗi.
Bankin ya kuma yi wasu gyare-gyare ga tsarin, inda ya ƙara tazarar da aka amince na aiki ga na’urorin PoS daga mita 10 zuwa mita 70.
A cewar sanarwar, “An ƙara iyakar tazarar Geo-Fence daga mita 10 zuwa mita 70, sannan an mayar da ranar fara aiwatar da dokar zuwa 1 ga Agustan 2026.”
Tsarin Geo-Fencing wata fasaha ce da ke tabbatar da cewa na’urar PoS tana aiki ne kawai a wurin da aka amince da ita. Wannan na taimakawa wajen sa ido kan mu’amaloli, rage damfara da kuma ƙarfafa tsaron tsarin biyan kuɗi ta hanyar lantarki.
Masana harkokin kuɗi sun bayyana cewa sabon tsarin zai taimaka wajen hana amfani da na’urorin PoS a wuraren da ba a yi musu rajista ba, tare da rage ayyukan masu damfara da ke amfani da irin waɗannan na’urori wajen aikata laifuffukan kuɗi.
CBN ya umarci dukkan cibiyoyin da abin ya shafa da su gabatar da hujjojin bin sabon tsarin kafin ko a ranar 31 ga Yulin 2026 ta hannun Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi.
Haka kuma, bankin ya buƙaci cibiyoyin kuɗi da su gaggauta warware duk wata matsala ta fasaha ko gudanarwa da ke tsakaninsu da Tsarin Canja Bayanai na ƙasa (National Central Switch) domin tabbatar da cewa aiwatar da sabon tsarin zai gudana ba tare da wata tangarda ba.
Masu lura da harkokin kuɗi sun ce ƙarin wa’adin zai bai wa masu gudanar da ayyukan biyan kuɗi damar sabunta tsarin su da kuma daidaita ayyukansu da sabbin ƙa’idojin CBN kafin fara cikakken aiwatar da dokar.
Ana sa ran matakin zai ƙara inganta tsaro da sahihancin mu’amalolin kuɗi ta hanyar lantarki a Nijeriya tare da rage yiwuwar aikata zamba a tsarin biyan kuɗi na zamani.
