Majalisar Dattawa za ta hanzarta kammala aikin dokar ‘yan sandan jihohi kan taɓarɓarewar tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa za ta fara aikin tabbatar da dokar kafa ‘yan sandan jihohi yayin da ta fara zamanta na yau Talata, kamar yadda Sanata Opeyimi Bamidele ya sanar a ranar Litinin.

Ya ce, jagorancin Majalisar Dokokin Ƙasa ya yanke shawarar ware dokar kafa ‘yan sanda da ainihin hanyoyin nazari akan kundin dokar ƙasa.

A cewarsa, suna haka ne don la’akari da halin da ‘yan Nijeriya ce ciki na rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ya sa suka sanya dukkan masu ruwa da tsaki aciki tun daga kan shugaban ƙasa har zuwa sauran masu faɗa a ji.

Ayyukan ‘yan bindiga, garkuwa da hare-haren ƙauyuka sun zama ruwan dare a Nijeriya, lamarin da ya sa fannin tsaro musamman na ‘yan sanda ke buƙatar sauyin salon gudanarwa.

Tun da jimawa gwamnoni suke neman a ba su damar iko da ‘yan sanda domin daƙile miyagun laifuka acikin al’umma akan lokaci.

Matuƙar aka sanya al’amarin acikin doka, zai zama babban sauyi a fannin tsaro a Nijeriya tun 1999.

By Babaji

Leave a Reply