Ƙaramar hukumar Katsina za ta horar da matasa 1,500 kan fasahar zamani

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Ƙaramar hukumar Katsina ƙarƙashin jagorancin Hon. Isah Miqdad AD Saude ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kamfanin Vision Pool Enterprises domin aiwatar da shirin Ilimin fasahar zamani da ƙirƙire-ƙirƙire na Katsina (KDLIP).

Shirin zai horar da kimanin matasa 1,500 kan ilimin kwamfuta, fasahar dijital, Artificial Intelligence (AI), kasuwancin zamani da kuma tsaron bayanai domin ƙara musu ƙwarewa da damar samun aikin yi ko dogaro da kai.

Wannan haɗin gwiwa na daga cikin ƙoƙarin ƙaramar hukumar Katsina na bunƙasa rayuwar matasa ta hanyar ilimi, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire.

Ana sa ran fara aiwatar da shirin nan ba da jimawa ba, wanda zai taimaka wajen gina matasa masu ƙwarewa da za su iya gogayya a duniyar fasahar zamani.

By ukarofi

Leave a Reply